Taron kasashe yan ba ruwammu yayi Allah wadai da Israila | Labarai | DW | 17.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashe yan ba ruwammu yayi Allah wadai da Israila

Wakilan kasashe 118 na kungiyar kasashe yan ba ruwammu sunyi Allah wadai da hare haren da Israila ta kai akan kasar Lebanon,sun kuma nuna goyon bayansu game da magance rikicin nukiliya na Iran cikin lumana.

Jawabin bayan taron daya hada kasashe da dama dake adawa da Amurka,ya kuma yi Allah wadai da aiyukan taaddanci,sai dai ya goyi bayan kungiyoyi masu fafutukar neman yancin da masu yaki da mamayar kasashensu.

Duk da cewa taron yace,demokradiya tsari na daya ya kamata kowace kasa tabi,amma bai kamata wani shiya ko wata kasa ta tilasta bin tsarin demokradiya irin nata ba.

Yawancin membobin kungiyar sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya data dauki mataki game da ikon da Amurka take da shi na darewa kujerar naki a cikin komitin sulhu na majalisar.