Taron kasashe renon Ingila a kasar Malta | Labarai | DW | 25.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashe renon Ingila a kasar Malta

Sarauniyar Ingila Elzabeth ta bude taron kasashe renon Ingila wanda ke gudana a birnin Valetta na kasar Malta. A jawabin ta, sarauniya Elzabeth ta yaba da akidar hadin kai da zumunta dake tsakanin daukacin kasashe 53 na kungiyar, tana mai cewa babban abin farin ciki ne yadda kasashen suka kasance tsinsiya madaurin ki daya . kasashen na Commonwealth wadanda suka kunshi alúmomi biliyan 1.8 wanda kuma ke zama kashi daya bisa biyar harkokin cinikayya a duniya a can baya sun kasance karkashin mulkin mallaka na kasar Britaniya. Taron na kwanaki uku wanda kasashen ke gudanarwa bayan shekaru biyu ana sa ran zai maida hankali akan muradun kasashe masu tasowa a game da shingen ciniki a taron hukumar cinikin ta duniya wanda zaá gudanar a birnin Hong Kong a watan Disamba mai zuwa.