Taron kasashe masu fada aji a duniya a game da rikicin Iran | Labarai | DW | 02.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashe masu fada aji a duniya a game da rikicin Iran

A yau ne wakilan kasashe shidan nan masu zaunanniyar kujera a kwamitin sulhu na Mdd, zasu gudanar da wani taro a birnin Paris na kasar Faransa.

Taron wanda ake sa ran zai sami wakilcin kasashen Amurka da Biritaniya da Faransa da Russia da kuma kasar Sin zai mayar da hankali ne wajen tattauna hanyoyin warware rikicin nukiliyar kasar Iran.

Wannan taro a cewar bayanai,ya kasance irin sa na farko a tun bayan da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta kai karar kasar ta Iran gaban Mdd, bisa karan tsaye da tayi ga umarnin ta na kin dai na sarrafa sanadarin Uranium.

Ya zuwa yanzu dai kasar Amurka tare da goyon bayan Biritaniya da Faransa na son ganin kwamitin sulhun ya dauki matakin ladaftarwa cikin gaggawa akan kasar ta Iran, to amma kuma a hannu daya kasashen Sin da Russia na da ra´ayi ne na ganin cewa an warware wannan rikici ta hanyar ruwan sanyi.

Rahotanni dai sun nunar da cewa wannan taron na a matsayin sharar fage ne ga taron ministocin kasashen masu fada aji a duniya, da ake sa ran gudanarwa a ranar 9 ga watan nan da muke ciki a can birnin New york na kasar Amurka.