Taron kare Muhali a Japan | Labarai | DW | 30.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kare Muhali a Japan

Ƙwararru daga ƙasashen Duniya sama da 200 sun cimma wata yarjejeniya ta kare halitu, da tsirai da kuma Dazzuzuka a Duniya

default

 Ministocin kula da kare muhali da kuma yanayi na sama da ƙasashe 200  sun cimma wata yarjejeniya ta kare halitu da kuma tsirai dake fuskantar barazanar ɓacewa a doran Duniya.Ministocin wanda suka cimma wannan shiri a ƙarshen taron da aka kammala a jiya a birnin Nagoya na ƙasar Japan bayan makonnin biyu na tattaunawa, sun fitar da wata sanarwa mai shafi 20 da ta tanadi  kare dazuzzuka da halitu, dakuma tsirai .

kafin nan da shekara ta 2020, tare kuma da tilasawa gwamnatocin ƙasashen kula da kiyaye ga shawarwarin da aka cimma.

Hubert Refuser Shugaban haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin dake fafutakar kare muhalli na nan ƙasar Jamus  ya shaida cewa wannan wata babbar nasara ce

Oton

 wannan mahawara wani mataki ne na farko kafin a kai ga gaci domin zai kara bada himma a Duniya

 na cewa mu duka  alhaki ya rataya a wuyanmu na yin wanin yunkuri a cikin ƙasashe masu tasowa da kuma waɗanda ke da arzikin masana'antu  akan wannan batu

Mawallafi:Abdourahamane Hassane

Edita       : Zainab Mohammed Abubakar