Taron Kara Wa Juna Ilimi Akan Guje-Gujen Hijira | Siyasa | DW | 05.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Kara Wa Juna Ilimi Akan Guje-Gujen Hijira

Alkaluma sun nuna cewar kimanin mutane miliyan 175 ne ke zama na kaka-gida a sassa dabam-dabam na duniya yanzu haka

Tutar Hukumar Taimakon Fasaha ta Jamus GTZ

Tutar Hukumar Taimakon Fasaha ta Jamus GTZ

A yanzu haka a nan kasar ta Jamus akwai ‚yan kaka-gida kimanin miliyan bakwai da dubu dari uku, a tsakaninsu akwai Serbiyawa dubu dari bakwai. Rukunin farko sun shigo nan Jamus ne a cikin shekaru 1960 domin ci rani. Tuni dai suka saje da takwarorinsu Jamusawa suna kuma taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin kasar. Alkaluma sun nuna cewar Serbiyawan na mallakar abin da ya kai Euro miliyan dubu 50 kuma su kan aiwatar da kimanin kashi 90% na kudadensu na shiga ne a nan Jamus. Bugu da kari kuma a duk shekara wadannan serbiyawa kan tura abin da ya kai Euro miliyan dubu daya zuwa gida, lamarin da taimakawa ga bunkasar tattalin arzikin Serbiya. Domin kuwa duka-duka abin da kasar ke samu na kudaden shiga akan abubuwan da take fitarwa zuwa ketare bai zarce Euro miliyan dubu biyu da dari uku ba a shekara. A lokacin da yake bayani game da haka gwamnan babban bankin Serbiya Radovan Yelasic cewa yayi:

Ko da yake yawa-yawancin kudin ana amfani da su ne wajen kyautata jin dadin rayuwar mutanen da lamarin ya shafa, amma a daya bangaren akan aiwatar da kashi 30 zuwa 40% a matsayin kudaden jari ko sayen kadarori kamar gidaje, wadanda ba su da wata nasaba da matsaloli na rayuwa.

Dukkan yankunan kasar Serbiya sun dogara ne kacokam akan wadannan kudade da ‚yan ci rani ko kuma ‚yan kaka-gida na kasar ke turawa gida daga nan Jamus. Shi kansa gwamnan babban bankin kasar ta Serbiya sai da ya rika tura Euro dari uku a kowane wata zuwa ga iyayensa a lokacin da yake zaune a nan kasar ta Jamus. Serbiya dai tana fama da tabarbarewar tattalin arzikinta, sannan ta fuskanci kaurace-kauracen kwararrun masana a tsakanin 1991 zuwa shekara ta 2000. A dai halin da ake ciki yanzu haka ma’aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa da sauran cibiyo na nan kasar sun fara gabatar da matakai, wadanda ake ganin zasu taimaka wajen dakatar da guje-gujen hijira na kwararrun masana da ma’aikata daga kasashe masu tasowa zuwa kasashe masu ci gaban masana’antu. A cikin wani bayani da tayi wata da ake kira Christiane Kuptsch daga kungiyar kodago ta kasa da kasa ta ce akwai kamfanonin Jamus da dama, wadanda ke ba da horo ga wadannan masu gudun hijirar a kasashensu. Akwai kuma shirye-shirye na hadin guiwa domin taimakawa wajen dakatar da wannan mummunan ci gaba.