1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kafofin yada labaru a Syria

April 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuMY

A yau ne aka bude taro na kasa da kasa na yan jarida dake kasashen larabawa da duniyar musulmi a Syria,taron da ake saran zai wanke kasashen larabawan dana musulmi a idanun kafofin yada labaru na kasashen yammacin turai.

Akwai wakilai kimanin 300 daga kafofin yada labaru na cikin gida dana kasashen ketare dake halartan wannan taro na yini uku ,wanda akayiwa lakabi da suna taron kafofin yada labaru na kasa da kasa dangane da bawa yankin palasdinawa goyon baya,wanda ke zama na ukun irinsa.

Taron wanda maaikatar harkokin yada labaru na kasar syria ta dauki nauyin gudanarwa zai duba tasirin kafofin yada labaru na kasashern larabawa,da marawa palasdinawa baya ,kana da duba irin rawa da kafofin yada labaru ke takawa wajen banbanta ayyukan tarzoma da yancin malla kan filaye.