1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kafofin yaɗa labaru

Awal(HON)June 2, 2008

Taron na duba rawar da kafofin yaɗa labaru ke takawa wajen samar da zaman lafiya da rigakafin rigingimu

https://p.dw.com/p/EBVn
Mista Bettermann yana jawabin buɗe taroHoto: DW

A yau ne a nan birnin Bonn aka buɗe taron ƙasa da ƙasa kan rawar da kafofin yaɗa labaru ke takewa wajen rigakafin rikice-rikice da samar da zaman lafiya a duniya. Taron na yini uku da ke samun halarcin wakilan kafofin yaɗa labaru daga kasashe fiye da 100, tashar DW tare da haɗin guiwar ofishin harkokin waje na Jamus da kuma wasu kamfanoni da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka ɗauki nauyin shiryawa. Mohammed Nasiru Auwal ya halarci bukin buɗe taron ga kuma rahoton da ya haɗa mana.◄


Kimanin ´yan jarida 800 da ´yan siyasa da masana ilimin kimiyya da masu fafatukar kare al´adu daga ko-ina cikin duniya suke halartar taron da aka sa masa taken Samar da zaman lafiya da rigakafin rigingimu. `Yan jarida suna sadaukar da rayukansu wajen gudanar da aikinsu. Alal misali a shekarun baya-bayan nan an yiwa wasu ma´aikatan DW biyu kisan gilla a Afghanistan. A jawabinsa na buɗe taron a cibiyar tarurruka na duniya dake cikin tsohon ginin majalisar dokokin Jamus dake nan Bonn, babban dakaraktan DW Erik Bettermann ya fara ne da nuna irin rawar da birnin Bonn ke takawa yanzu a matsayin wata cibiya ta kafofin yaɗa labaru a Jamus. Wannan taro ya na mayar da hankali ne kan lalubo hanyoyin tuntuɓar juna don samun zaman lafiya inji mista Erik Bettermann.


Ya ce "Ya zama wajibi a tattauna a kuma fayyace rawar da ´yan jarida da kafofin yaɗa labaru ke takawa. Hakan ya haɗa da kangarkin rikice-rikice da samar da zaman lafiya, samar da kyakkyawan shugabanci da kare haƙin bil Adama da ba da ilimi mai nagarta da kuma ci-gaban ƙasa."


Shin mai nahiyar Turai ke yi don magance tashe tashen hankula a duniya? Wannan dai ita ce tambayar da ake mayar da hankali kanta a muhwawwarorin da ake yi a taron. Tun fil azan batun rigakafin rigingimu ke zayyane a cikin ginshiƙan manufofin ƙetare na ƙungiyaar tarayyar Turai. Sojojin EU ƙarƙashin Majalisar ɗinkin duniya suka tabbatar da tsaro a zaɓen Kongo yayin da ´yan sandan ƙungiyar kuma ke kula da kan iyakar Masar da Zirin Gaza. A ƙasashe kamar Afghanistan da na yankin Balkan EU na taimakawa a aikin sake gina waɗannan yankuna tare da girke mulkin demoƙuraɗiya. To sai dai a lokuta da dama ana gaza cimma manufar da aka sa gaba inji karamin sakatare a ma´aikatar harkokin wajen Jamus Georg Boomgarden.


Ya ce "´Yancin yaɗa labaru shi ne sharaɗin farko na samun wani tsarin demuƙuraɗiya da zai yi aiki. Ba shakka ´yancin faɗar albarkacin baki da girmama juna na taka muhimmiyar rawa wajen kawad da halayya ta ƙyamar juna."


Ita kuwa a jawabinta ´yar Iran ɗin nan da taɓa samun kyautar zaman lafiya Dr. Shirin Ebadi ta taɓo rawar da ´yan jarida ke takawa ne a ƙasarta. Wakilin sashen Hausa a Maiduguri Salisu Babangida Jibril na daga cikin mahalarta wannan taro na tambaye shi yadda ya ga taron.