TARON JUYAYI NA KWAMITIN AUSCHWITZ | Siyasa | DW | 25.01.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TARON JUYAYI NA KWAMITIN AUSCHWITZ

A birnin Berlin, an gudanad da taro don tunawa da cika shekaru 60 da `yanto sansanin nan na Auschwitz, da kuma juyayin wadanda suka rasa rayukansu a sansanin. Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Gerhard Schröder, ya yi wa taron jawabi.

Shugaba Schröder a lokacin da yake yi wa taron juyayi kan sansanin Auschwitz jawabi a birnin Berlin

Shugaba Schröder a lokacin da yake yi wa taron juyayi kan sansanin Auschwitz jawabi a birnin Berlin

A cikin jawabinsa ga taron kwamitin Auschwitz, mai kula da makoman wadanda aka ceto su da ransu daga sansanin gwale-gwalen nan da Hitler ya kafa, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Gerhard Schröder, ya karfafa cewa, alhakin miyagun laifuffukan da Hukmar mulkin Nazi ta aikata a lokacin yakin duniya na biyu, har ila yau yana rataye a wuyar Jamus, kuma wajibi ne a dinga tunawa da irin wannan mummunan aikin.

"Ina bayyana matukar nadamata ga wadanda aka halaka, kuma gareku, wadanda kuka yi arzikin fitowa daga wannan jahannama ta sansanin gwale-gwale da ranku. Sansanoni dai kamar Chelmo, da Belzec, da Soibor, da Treblinka, da Maidanek da Auschwitz-Birkenau, dukkansu sunaye ne wadanda har abada ba za a taba mantawa da su ba a tarihin Jamus da ma na Turai gaba daya, da kuma a tarihin wadanda suka sha azaba a cikinsu. A wannan lokacin juyayi dai, muna bakin ciki, kuma da gaske ne za mu dau nauyin da ya rataya a wuyarmu."

Ga shugaba Schrödern dai, babban nauyin da ya rataya a wuyar Jamus a halin yanzu, shi ne daukan duk matakan da suka dace wajen yakan masu nuna kyama ga akidar Yahudanci da kuma yunkurin farfado da manufofin Nazi. A cikin jawabinsa dai, shugaban gwamnatin, ta tarayyar Jamus, ya yi matashiya ne da tabargazar baya-bayan nan da ta barke a majalisar dokokin jihar Sachsen, inda `yan jam’iyyar NPD, masu bin tsatsaurar ra’ayi, suka kaurace wa shirin juyayin da aka tsara don girmama rayukan da suka salwanta karkashin mulkin Nazi. Ya kara da cewa:-

"Wajibi ne ga duk `yan dimukradiyya, da su hada giwa wajen huskantar kalubalantar da azzaluman Nazi ke yi musu. Duk abokan gaban dimukradiyya da masu nuna kyama ga bambancin jinsi ko na addini, to bai kamata su sami wata madafa ba, a ko’ina inda ake tafiyad da dimukradiyya".

Su dai wadanda suka tsira da ransu daga wannan sansanin, sun bayyana nadamarsu game da mantuwar da ake yi wa wannan lamarin da ya shafe su. Kamar yadda shugaban kungiyar Yahudawa ta Duniya, Israel Singer ya bayyanar, kusan fiye da rabin mutanen da aka yi musu tambayoyi a Birtaniya ne suka bayyana cewa, ba su taba jin sunan Auschwitz ba.

"Akwai dai gidajen tarihi, da Taruka da kuma ababan tuntuni da ake da su a ko’ina game da wannan kisan kiyashin. Amma ban da `yan siyasa da Yahudawa da abokansu, babu mai kai musu ziyara. Mafi yawan jama’a sun fi gwammacewa su kasance cikin duhu."

Wani wakilin matasan da iyayensu ko kuma kakkaninsu suka sha azaba a sansanonin, shi ma ya yi wa taron jawabi. Artur Brozowski, mai shekaru 21 da daya da haihuwa, wanda a halin yanzu dalibi ne a kasarsa ta Poland, ya bayyanna cewa, an taba tsare kakansa a sansanin Auschwitz, inda a nan ne kuma ya mutu. Saboda hakan ne dai ya sa ya koyi Jamusanci don ya iya ba da tasa gudummuwa wajen fahimtar juna.

Duk masu jawabi a bikin juyayin na yau dai sun nanata muhimmancin da akwai ne, na kada a yi sake har matasa su manta da wannan mummunan aikin da ya gudana a sansanin Auschwitz. Shugaba Schröder, ya ce bai kamata a sake a bari hakan ya auku ba.

 • Kwanan wata 25.01.2005
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvdU
 • Kwanan wata 25.01.2005
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvdU