Taron Isra´ilawa da Palestinawa a Tokiyo | Labarai | DW | 14.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Isra´ilawa da Palestinawa a Tokiyo

Tawagogin Isra´ila da na Palestinu sun buɗa zaman taro a birninTokyo, da zumar cimma warwaae taƙƙadama a tsakanin su.

Za a gudanar da wannan taron yini 2, bisa jagorancin hukumomin kasar Japon ,da su shiga wani saban yunƙurin na daidaita al´ammura a yankin gabas ta tsakiya.

Wani baban buri da mahalarta taronke buzkatar cimma shine da bunkasa saye da sayarwa tsakaninkasashen 2 masu gabada juna, tare da shinfiɗa matakan zaman lahia na wanzuwar wanann cinaki.

Taron ya biwo bayan alƙawarin da tsofan praministan ƙasar Japon, Junichiro Koizumi ya ɗauka, a lokacin da ya kai ziyara yankin a watan juli na shekara da ta gabata.

A loakacinda su ka gabatar da jawabai shugabanin tawagogin 2, sun bayyana aniyar tantanawa cikin fahintar juna, da zuma cimma burin da aka sa gaba.

To saidai hausawa kance wai, an jimma a na tabka ruwa, ƙasa ta na shanyewa.