1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron inganta matakan tsaro a Munich

February 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuS1

Sakataren tsaron Amurka Roberts Gates ya karyata zargin da shugaba Vladimir Putin na Rasha yayi wa washinton na ruruta wutan rikicin sabbin makamai.Mr Gates yayi wannan furucin ne ayayinda yake jawabi a wajen taron kasa da kasa kann harkokin tsaro a birnin Munich dake nan jamus.Ya bayyana cewa dole ne wakilan kungiyar tsaro na kasashe yammaci ta Nato,suyi aiki kafada da kafada da kasar Rasha kann harkokin tsaro.Wadannan kalamai nasa sunzo yini ,bayan shugaban na Rasha a wannan taro na matakan tsaro,ya fadawa mahalarta cewa Washinton na nuna halin karfion makamai akan wasu kasashe,batu dake tilasta kasashe da basuz da karfi neman makaman nuclear domin kare kansu.Dayake jawabi a kasar Saudi Arabia dake zama kafarsa ta farko a rangadin aiki daya fara a yankin gabas ta tsakiya,shugaba Vladimir Putin yace manufiofin Amurka a Iraki sun gaza cimma komai,face jefa kasar cikin haki na kakanikayi na rayuwa.Ya bukaci Washinton data tsara yadda zata fara janye dakarunta daga cikin kasar ta Iraki.