1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hukumar majalisar Dinkin Dunia mai yaki da yaduwar makamman nuklea a game da rikicin Iran

February 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9o

Nan gaba a yau ne, hukumar yaki da yaduwar makaman nuklia ta Majalisar Dinkin Dunia, zata, zaman taro, domin tantana batu mai sarkakkiya,na gurfanar da Iran, gaban komitin sulhu na majalisar Dinkin Dunai.

A ranar jiya laraba, kasashe 5, masu kujerun dindindin ,a komitin sulhu tare da Kasar Jamus, su ka kamalla shirya takardun hadin gwiwa, na bukatar wannan komiti, ya dauki matakin gurfanar da Iran, domin ladabtar da ita, a sakamakon, taurin kunnen da ta nuna, na burjenewa kasashen dunia, da su ka bukaci, ta yi watsi da aniyar ta, ta kera makaman nuklea.

A nasu bangaren hukumomin Iran, sun gargadi kasashen da cewar, muddun su ka gabatar da kara, gaban komitin sulhu, to Iran kuwa, ta kare bada hadin kai ga tantanawar warware wannan matsala.