1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hukumar kare haƙƙoƙin bani adama a birnin Geneva

September 18, 2006
https://p.dw.com/p/Buj5

Yau ne Majalisar kare haƙƙoƙin bani Adama ta Majalisar Dinkin Dunia, ke shirya zaman taron ta na 2,a birnin Geneva na kasar Suizland.

A tsawan makwani 3, ƙasashen membobin Majalisar, za su tantana batutuwa daban daban, da su ka shafi halin da dunia ke ciki, ta fannin yancin bani Adama.

A makon farko, za su saurari rahotanin da su ka tattara daga sassa daban daban na dunia, da su ka jiɓacin wariyar launin fata, anfani da ƙananan yara cikin yaƙe- yaƙe, da kuma matsalar shara mai guba, kamar irin wadda a ka zubda a farkon watan da mu ke ciki a kasar Cote d´Ivoire, waddda kuma tayi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 6,da jikata wasu ƙarin dubanan jama´a.

Kazalika mahalarta wannan taro, za su shata tsarin ayyuka na tsawan watani 12 ma su zuwa, ga komiti mai kulla da yancin da aka girka a watan yuni da ya wuce.

Saidai tunni saban komitin ya fara samun suka, a game faɗawa cikin yanayin ko in kulla, da tsofan komitin ya nuna ga ƙasashen da ake zargi da ƙuntatawa jama´a.

A game da haka, shugaban sabuwar Majalisar kare haƙƙoƙin jama´a ta Majalisar Dinkin Dunia Louis Alfanso de Alba ya maida martani kamar haka:

„I na kyauttata zaton sabuwar hukumar zata taka rawar gani, ta fannin cimma burin da a ka sa gaba, ta la´akari da cewa, dukan ƙasashe membobin ta sun ɗauri kyaukyawar aniya.

Kuma bama za yiwu ba, a cenza tsari, da sallon tafiya, kuma a koma gidan jiya noman goje.“