Taron hukumar IAEA akan Iran a gobe litinin | Labarai | DW | 05.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron hukumar IAEA akan Iran a gobe litinin

Ministan harkokin wajen kasar Sin Li Zhaoxing yayi kira ga magabatan kasar Iran dasu amince da komawa tattaunawa da Rasha da kungiyar gamayyar turai a dangane da batun Nuclear kasar,gabannin babban taron hukumar kula da harkokin Nuclear na mdd.

A gobe litinin ne Wakilan gudanarwa 35 na hukumar IAEA,zasu gudanar da taron da zai jagoranci komitin sulhun mdd ta dauki matakan ladabtarwa akan Tehran.Ministan Sind in ya jaddada cewa ,warware wannan rikici na Iran ta hanyar Diplomasiyya shine mafi aalla wa ita da sauran kasashen duniya da ita mdd.Iran dai ta sha nanata cewa tana gudanar da harkokin nuclearnta ne ba da wata mummunar manufa,face samarwa alummarta ingantaccen wutan lantarki.Ayayinda kasahen Faransa da jamus da Britania sukace bata gabatar da wani sahihin bayanai a taron da akayi da ita a makon dai gabata da zai tabbatar da wannan manufa nata ba.Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana cewa taron na hukumar Nuclear a gobe,zai bada damar sake cigaba da tattaunawa da Iran ko kuma a gurfanar da ita gaban komitin sulhun mdd.