Taron Holocaust a Tehran | Siyasa | DW | 11.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Holocaust a Tehran

Gwamnatin Iran ta kira taron yini biyu akan ta'asar Holocaust a fadar mulki ta Tehran

Makonni kalilan bayan rantsar da shi da aka yi a matsayin sabon shugaban kasar Iran a wajejen tsakiyar shekarar da ta gabata ta 2005, shugaba Ahmadinajad yake zargin kasashen Birtaniya da Amurka da sanya wa kasarsa karan-tsana, amma ya ce babbar uamal’aba’isi ita ce Isra’ila, kamar yadda aka taba ji daga madugun juyin-juya-halin Iran Khumeini. A yayinda a zamanin baya a karkashin mulkin Shah kasar Iran ke hulda ta kut da kut da Isra’ila, nan da nan al’amura suka canza inda Isra’ilar ta zaza babbar abokiyar gabar Iran bayan juyin juya halin Islamar kasar, shi kuma Ahmadinajad ke bayyana fatan kawar da kasar ta Yahudawa daga doron kasa. A ganinsa an kafa Isra’ilar ce akan turbar karya, inda aka kago tatsuniyar nan ta Holocaust domin shigar da Isra’ilar a tsakanin kasashen Musulmi. Ya ce idan har da gaske ne an yi farautar Yahudawan to kuwa ashe wajibi ne kasashen dake da wannan alhaki na ta’asa, wato Jamus da Austriya su dauki nauyin Yahudawa su kuma shere musu wajen zama a harabar kasashensu. Wadannan kalamai na shugaban kasar ta Iran ya harzuka jama’a a sassa daban-daban na duniya. Shi kuma shugaban Yahudawa tsiraru a kasar Iran Haroun Yashayaei ya dauki wani mataki na ba zata, inda ya rubuta wasika zuwa shugaba Ahmadinajad yana mai bayyana rashin jin dadinsa akan wadannan lafuzza. Ya ce ta’asar Holocaust na daga cikin munanan laifukan da bdan Adam ya fuskanta a cikin tarihinsa a karni na 20, a saboda haka ta yaya za a sa kafa a yi fatali da ire-iren kisan kiyashi da fatattakar Yahudawa da aka yi a nahiyar Turai a lokacin yakin duniya na biyu. To sai dai kuma Ahmadinajad bai amsa wasikar ba, a maimakon haka sai ya ba da gudummawar kudi don taimaka wa wani asibitin Yahudawa dake Tehran, amma ya ci gaba da kalubalantar Isra’ila yana mai saka lada ga duk wanda ya lashe wata tserereniyar da ya shirya na zanen kagen Holocaust da kuma shirya wannan taron na yini biyu a birnin Tehran wai domin tattaunawar gaggan masana 67 daga kasashe 30. Ga dai abin da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Hamid-Reza Asefi yake cewar:

“Holocaust ba wani lamari ne mai tsari da ba za a iya tabo maganarsa ba. Wajibi ne a tattauna a kuma bi diddigin lamarin daga tushensa. Kawo yanzun dai ba a san tahakikanin wadanda zasu halarci taron ba. Kuma ko da yake kakakin ma’aikatar harkokin wajen yayi ikirarin cewar za a tattauna ne tsakani da Allah, amma fa ko kadan ba za a amince da wani ra’ayin da ya banbanta da na gwamnatin Iran ba, kuma a saboda haka koma gayyatar masu banbancin ra’ayin ba za a yi.