Taron hanyoyin shawo kan dumamar yanayi a Bangkok | Labarai | DW | 30.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron hanyoyin shawo kan dumamar yanayi a Bangkok

Kwararru ta fannin kula da yanayi sun hallara a birnin Bangkok din kasar Thailand ,domin nazarin hanyoyi da zaa bi na rage illolin karuwar dumamar yanayi ,tsaka tsakin sabanin raayi dake da akwai adangane da yadda zaa shawo kann wannan matsala.

Akalla akwai kwararru ta fannin kimiyya 400 da wasu kwararru ta fannin yanayi daga kasashe 120,dake halartan wannan taro na makon guda ,wanda ke zama na ukun irinsa ,akarkashin hukumar nan ta mdd dake kula da dumamar yanayi ta kasa da kasa ,watau IPCC atakaice.

Rahotanni biyu da aka gabatar dangane da taruruuka biyu da suka gudana makamancin wannan dai,sunyi gargadi dangane da karuwar matsalar dumamar yanayi,da kuma irin illoli da zai haifar da suka hadar da fari da ambaliyan ruwa da guguwa mai karfi ,da kruwan yunwa da bazuwan cututtuka.

Ana saran fitar da sakamako na uku a karshen wannan taron a ranar jumaa.