Taron haɗin kan Somalia ya watse baran-baran | Labarai | DW | 15.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron haɗin kan Somalia ya watse baran-baran

Mahalarta taron haɗin kan ƙasa a Somalia, sun watse baran-baran.

Jim kaɗan bayan buɗe taron, wasu tiƙa -tiƙan gurnetoci su ka farfashe, gap ga babban opishin yan sanda, inda a ke gudanar da mahaurorin.

Ya zuwa yanzu, babu cikkaken bayyani, a game da yawan mutanen da su ka rasa rayuka, kokuma su ka ji ranuka bayan kai wannan hari.

Gurnetocin sun tarwatse, a daidai lokacin da shugaban ƙasa Abdullahi Yusuf Ahmed, ke gabatar da jawabi ga mahalarta taron.

Kamin ya kammalla wannan jawabi, jagoran taron ya buƙaci ɗage shi, har ranar alhamis mai zuwa.

Cemma dakarun kotunan Islama, da su ka ƙi amsa goran gayyata, sun alkawarta sa tarnaƙi ga gudanar taron haɗin kan ƙasar, wanda a cewar su, ba shine hanyar samar da zaman lahia ba, a ƙasar Somalia.

Dakarun kotunan Islama, sun bayyana hallarta taron amma da sharaɗin a shirya shi, a wata ƙasa daban,kuma bayan dakarun Ethiopia sun fita daga Somalia.

Yau shekaru 16 kenan daidai da tashe-tashen hankula ke ci gaba da ɗaiɗaita ƙasar Somalia.