Taron haɗin-gwiwar tsaro a Turai | Labarai | DW | 01.12.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron haɗin-gwiwar tsaro a Turai

Ƙungiyar Haɗin-gwiwar tsaro a Turai(OSCE) ta fara wani taro a ƙasar Kazakhstan.

default

Zauren manema labaru a taron OSCE a Astana babban birnin Kazakhstan

A karon farko cikin sama da shekaru goma, Ƙungiyar Hadin-gwiwar tsaro ta nahiyar Turai, OSCE na gudanar da taro a ƙasar Kazakhstan. Wannan taro da ke samun halartan shugabanni irinsu Angela Merkel ta Jamus, da Dmitry Medvedev na Rasha da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Ban Ki-moon da Hilary Clinton, sakatariyar harkokin wajen Amirka, manufarsa ita ce warware rikice-rikicen da ake fama da su a faɗin Turai da tsohuwar Tarayyar Soviet. An tsaurara matakan tsaro a Astana babban birnin ƙasar ta Kazakhstan a daidai lokacin da wakilai ke hallara domin shawarta halin da ke wakana a Afganistan, da sauran rikice-rikice da aka daɗe ana fama da su da kuma hanyoyin kau da ayyukan tarzoma da fataucin miyagun ƙwayoyi. Ƙungiyar Human Rights Watch da ke da mazauninta a birnin New York na ƙasar Amirka dai ta yi suka game da gudanar da taron a wannan ƙasa ta nahiyar Asiya wadda a cewarta ba ta samu wani ci gaba mai ma'ana ba a dangane ga kare haƙƙin bil Adama.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Yahouza Sadissou Madobi