Taron haɗin ƙasar Libanon a France | Labarai | DW | 15.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron haɗin ƙasar Libanon a France

Wakilan ɓangarori daban daban na ƙasar Libanon sun kammala zaman taron yini 2, a kussa da birnin Paris na ƙasar France.

Maƙasudin wannan taro, shine ci gabada lalubo matakan warware rikicin siyasa,da ya ƙi ci ya ƙi cenyewa a wannan ƙasa.

Tun watan november na shekara ta 2006, ƙasar Libanon, ta tsunduma cikin wani halin tsaka mai wuya na siyasa, bayan murabus ɗin ministocin Hizbullahi, da na jam´iyun adawa masu ɗaurin gidin Syria.

Idan ba a warware wannan rikicin ba , masharanta a kann harakokin siyasar ƙasar na nunar da cewa akwai matuƙar wuya a cimma nasara shirya zaɓen shugaban ƙasa a watan September mai zuwa, kamar yadda a ka tsara da farko.

Ministan harakokin wajen France, Bernard Kouchner da ya jagoranci wannan taro, ya bayyana gamsuwa a game da saka makon da ya cimma, saidai ya ƙara da cewar har yanzu akwai sauran rina kaba, wajen kai ga burin da a ka sa gaba.

A nasa ɓangaren ministan tsaron France Herve Morin,ya kai ziyara yini ɗaya, a ƙasar Libanon inda ya bayyanawa Praministan Fouad Siniora, goyan bayan hukumomin Paris, a game da yunƙurin kawo ƙarshen tashe-tashehn hankula a Libanon.