1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron girmama Nelson Mandela

December 10, 2013

Shugabannin ƙasashen duniya da 'yan Afirka ta Kudu sun hallara a filin wasan Johannesburg don gudanar da jawabai na girmama tsohon shugaban ƙasar Nelson Mandela.

https://p.dw.com/p/1AWH1
Nelson Mandela Zeremonie Beisetzung Stadion Junge Plakat
Hoto: Reuters

Da misalin ƙarfe goma na safe ne aka fara taron daidai lokacin da ake yin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya inda shugabannin duniya ke ci gaba da yin jawabai na girmama wa da kuma yin waiwaye na irin rayuwar da Mandela ya gudanar. Lokacin da ya ke jawabinsa wajen taron sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon cewa ya yi ''Afirka ta yi asarar gwarzo, an yi asarar uba kana duniya ta yi asarar aboki. Nelson Mandela ya wuce guda daga cikin manyan shugabannin da duniya ta taɓa samu, makaranta ce mai zamana kanta.''Baya ga Ban Ki-Moon da ya yi jawabi wajen taron, shugabanni irin su Barack Obama na Amirka da shugaban Kyuba Raul Castro da shugaban India Pranab Mukherjee gami da shugaba Afirka Kudu Jacob Zuma sun yi nasu jawaban.

Sauran shugabannin da ke wajen taron wanda ke ci gaba da gudana sun haɗa da firaministan Burtaniya David Cameron da Francois Hollande na Faransa da shugaban Robert Mugabe na Zimbabwe gami da ƙarin wasu shugabannin duniya sama da guda 90

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane