Taron gangamin tunawa da Rabin a Tel Aviv | Labarai | DW | 13.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron gangamin tunawa da Rabin a Tel Aviv

Kimanin mutane dubu 200 ne suka halarci wani taron gangami a birnin Tel Aviv don tunawa da tsohon FM Isra´ila Yitzhak Rabin wanda aka yiwa kisan gilla shekaru 10 da suka wuce. Wani Bayahude mai tsattsauran ra´ayi dake adawa da shirin wanzar da zaman lafiya ya harbe FM har lahira. Tsohon shugaban Amirka Bill Clinton wanda ya halarci gangamin ya yabawa karfin zuciyar da Rabin ya nuna don amfanin Isra´ilawa da Falasdinawa. Wannan bikin dai ya zo daidai da bukukuwan da ake yi a Zirin Gaza na zagayowar shekara daya da rasuwar shugaban Falasdinawa Yasser Arafat. Rabin da tsohon ministan harkokin wajen Isra´ila Shimon Peres da kuma Arafat sun taba samun kyautar Nobel ta zaman lafiya saboda rawar da suka taka wajen shirya yarjejeniyar birnin Oslo.