1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G8 a Saint-Petesburg na ƙasar Russia

Yahouza S.MadobiJuly 15, 2006

Ƙasashe 8 mafi ƙarfin tattalin arziki a dunia sun buɗa taro a birnin Saint-Petesburg na ƙasar Russia

https://p.dw.com/p/Btz8
Hoto: AP

Shugabanin ƙasashe da na gwamnatoci 8, masu ƙarfin tattalin arziki a dunia, na ci gaba da zaman taro, a birnin Saint-Petesburg na ƙasar Rasha.

Jiya ne aka buɗa wannan taro da wata gagaramar liyafar cin abinci, a hamshaƙen dandalin Konstantin, da ke gaɓar teku.

Shugaban ƙasar Rasha Vladmir Poutine, da takwarorin sa, na ƙasashen Amurika, France, Jamus, Britania, Italia, Japon da Kanada, sun fara tantanawa gadan-gadan a yau lahadi a game da mahimman batutuwa masu nasaba da diplomatia da kuma tattalin arzikin a dunia.

Saidai taron na wakana a daidai lokacin da yankin gabas ta tsakiya ya tsunduma cikin yanayin yaƙi, a sakamakon hare hare babu ƙaƙƙabtawa da Isra´ila ke ci gaba da abkawa Labanon, da zirin Gaza.

Kussan kacokam, wannan batu, ya mamaye ajendar taron G8.

Ƙasashen guda 8 mafi karfintattalin arziki a dunia,na fuskantar rarrabuwar kanu, a kan matakin magance wannan rikici.

A ganawar da shugaban ƙasar Amurika Georges Bush yayi da shugaban Rasha Vladmir Poutine, ya dra alhakin barkewar rikicin ga Kungiyar Hezbollah, Bush ya ce :

Babbar hanyar samun massalaha itace:.

Idan a a kayi waiwaye adon tafiya, za a fahinci cewar Yaƙin ya ɓarke, bayan da Hezbollah ta harba rokoki zuwa Isra´ila sannan ta capke sosjoji 2.

Wannan shine tushe matsalar.

A kan haka, hanya ɗaya tilo ta warware ta, itace Hezbollah ta ajje makamai, ta kuma daina kai hare hare zuwa Isra´ila.

Don cimma wannan mataki ina kira, ga Syria ta sa baki, ta la´kari da dangatakar ta, da ƙungiyar Hezbollah.

A nasa gefe, shugaban ƙasar Rasha, ya nuna rashin amincewa da wannan hujjojin da shugaban Amurika ya bada.

Ƙarara Poutine ya nuna rashin gaskiyar gwammnatin Isra´ila, duk da cewar itama Hezbolah da nata leffin.

A taƙaice, an samu mattuƙar rabuwar kanu, da rashin fahinta tsakanin shugabanin 2, a dangane da matsalar.

Shima shugaban ƙasar France, Jaques Chirac, ya bayyana matuƙar takaici, ga hare haren kan mai uwa da wabi, da Isra´ila ke kaiwa, zuwa Labanon.

Chirac ya yi kira ga shugabanin G8, da su yi iya ƙoƙarin su, domin dakatar da wannan yaƙi, da ke tamkar gama ƙawai da dutsi, ta la´kari da dimɓin makamai ,da hare hare, ta sama, ta ruwa,da ta ƙasa, da Isra´ial ke ci gaba da abkwa Labanon.

Ko da Hezbollah ta kai hari zuwa Isra´ila, martanin da Isra´ilawa su ka maida, inji shugaban ƙasar France, ya wuce gona da iri.

Bayan batun yankin gabas ta tsakiya, shugabanin G8, za su tantana a kan sauran batutuwa da su ka shafi makaman nukleyar Iran, da makamai masu lizzami, da Korea ta Arewa ta harba makon da ya gabata gabata.

Harakokin da su ka shafi tattalin arziki, da cuwarwarta a ƙasashen masu tasowa, bisa dukkan alamu ba za su yi tasiri ba, a taron, dalili da halin rikici, da dunia ta tsinci kanta ciki,a yan kwanakin nan.

Gobe idan Allah ya kai mu, shugabanin ƙasashe masu tasowa da su ka haƙa da na China, India, Brasil, Mexico, Afrika ta kudu, Kongo ,da Kazakhstan za su issa birnin Saint Petesburg, domin tantanawa da shugabanin G8, a kann batutuwan daban-dabanda su ka jiɓanci hulɗoɗi tsakanin ɓangarorin 2.