1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G20 ya karkata ga kasuwanci da tsaro

Yusuf Bala Nayaya
July 8, 2017

Taron da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke karbar bakunci ya samu halartar shugabanni irinsu Donald Trump da Vladimir Putin da ma wasu shugabanni daga kasashen Tarayyar Turai da yankin Asiya.

https://p.dw.com/p/2gBcf
G20 Hamburg Trump Merkel Tusk
Hoto: Reuters/I.Langsdon

A wannan rana ta Asabar ce shugabanin kasashe ke sake zama a rana ta biyu inda za su tattauna kan batun kasuwanci da sauyin yanayi da yaki da ta'addanci a duniya, abin da ke zuwa a taron koli na birnin Hamburg na Tarayyar Jamus, taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da masu adawa da tsarin duniya bai daya ko "Anti-globalization" a turance ke ci gaba da karon batta da 'yan sanda.

Taron da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke karbar bakunci ya samu halartar shugabanni irinsu Donald Trump da Vladimir Putin da ma wasu shugabanni daga kasashen Tarayyar Turai da yankin Asiya. Merkel dai ta ce dole shugabannin su cimma matsaya kan batutuwa kafin sakamakon taron ya samu karbuwa.

Wasu manyan batutuwa a taron na zama yadda za a kulla danganataka ta kasuwanci tsakanin kamfanoni na kasashen masu ci gaban masana'antu da kasashen Afirka kana za a duba batun 'yan gudun hijira da kuma lafiya.