1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron farko na Majalisar Ministocin Hamas

April 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2y

Yau ne sabuwar majalisar ministocin Hamas, ke zaman taron ta na farko.

Wannan taro, ya zo kwana ɗaya rak, bayan da saban ministan harakokin wajen Palestninu, Mahmud Zahar, ya rubuta wasiƙa zuwa ga Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Dunia, wace a cikin ta ya bayyana aniyar Hamas ta bada haɗin kai, domin samar da zaman lahia mai ɗorewa ,tsakanin Palestinu da maƙwabtan ta.

Masharahanta a yankin gabas ta tsakiya, na ci gaba da passara wannan kalma, ta Maƙwabta.

Bisa dukkan alamu, kalmar na nuna cenji akida ga Hamas, ta hanyar amincewa da Israela,a matsayin yanttantar ƙasa.

Har ya zuwa gabanin rubuta wannan wasika, Israela na zaman haramtaciyar kasa, ga ƙungiyar Hamas.

Wakilin Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin gabas ta tsakiya, ya ƙi yace komai, a game da wasikar ta ministan harakokin wajen Palestinu.

Saidai a wani shafi na wasiƙar, Mahmud Zahar ya nunar da cewa, matakin ƙarfin soja,da Isra´ila ke ci gaba da ɗauka, a yankunan Palestinawa, na iya kawo ƙarshen yiwuwar samar da zaman lahia a yankin.