Taron farko na majalisar kasar Somalia | Labarai | DW | 26.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron farko na majalisar kasar Somalia

A yau ne majalisar wucin gadi ta kasar Somalia ta fara zamanta na faro a cikin kasar ta Somalia,tun komowarta gida daga gudun hijira da takeyi a kasar Kenya a shekarar data gabata.

Shugaban majalisa Sharif Hassan Sheikh Adan,yace an bude zaman majalisar ne a birnin Baidoa wanda keda tazarar kilomita 250 daga birnin Mogadishu,inda yan majalisa 205 da kuma shugaba Abdullah Yusuf Ahmed da Firaminista Ali Muhammad Gedi suke halarta.

Gwamnatin ta wucin gadi,da aka kafa a karshen 2004,itace ta 14,a kokarin kasar Somalia na kafa gwamnatin tsakiya a kasar da yaki ya tagaiyara kuma babu cikakkaiyar gwamnati tun 1991,bayan hambarar da gwamnatin muhamad Siad Barre.

Ana dai sa ran yan majalisar zasu kara sabunta bukatarsu ta neman karin agaji ga miliyoyin jamaar kasar da suke fuskantar fari da yunwa a kasar.