Taron Faransa da ƙasashen Afirka | Labarai | DW | 30.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Faransa da ƙasashen Afirka

ƙungoyoyi kare hakkin jama'a sun fara sukan manufofi taron da Faransa za ta gudanar tsakaninta da ƙasashen Afirka.

default

Shugabannin Afrika da takwaransu na Faransa kan teburin tattaunawa

Ƙungiyoyin kare hakkin bil Adama sun fara tayar da jijiyoyin wuya dangane da bai wa shugabannin Afirka da suka yi ƙaurin suna damar halartar taron da Faransa za ta gudanar daga gobe litinin tsakaninta da ƙasashen Afirka. Ƙungiyar Human Right Watch ta nunar da cewa bai kamata ƙasar ta Faransa ta buɗe ƙofofinta ga shugabanin na Afirka da suka yi fice a fanninn take haƙƙin jama' a ba.

Daga cikin shugabannin da ƙungiyoyin ke adawa da halartansu taron har da firaministan Habasha Meles Zenawi, da shugaban ƙasar Kwongo Brazaville Denis Sassou NGuesso ,da ma dai shugaban riƙon ƙwarya na Guinee Conakry wato Sekouba Konate. Ƙungiyoyin har ila yau sun yi Allah wadai game da rashin tsinana wani abin azo a gani da taron tsakanin Faransa da Afrika ba yayi.

Wannan dai shi ne karon farko da Nicholas sarkozy zai jagoranci taron tun bayan ɗarewarsa kan karagar mulki. Batun matsin tattalin arziki da duniya ke fiskanta ne, zai mamaye taron da ke zama irinsa na 25 tsakanin Faransa da ƙasashen na Afirka.

Mawallafi: Mohammed Auwal Balarabe

Edita: Halima Balaraba Abbas