Taron EU da Iran a birnin Ankara | Labarai | DW | 25.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron EU da Iran a birnin Ankara

Yau ne a birnin Ankara na ƙasar Turquia a ka koma tebrin shawarwa tsakanin ƙungiyar Taraya Turai da Iran, da zumar cimma matsaya ɗaya a kan batun rikicin makaman nuklea.

Sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai, Havier Solana, da shugaban tawagar Iran Ali Larijani, za su bitar inda aka kwana, a cikin wannan taƙƙadama, da kuma ci gaba, da lalubo sabin hanyoyin kai ga masalaha.

Babban burin da su ka gaba a wannan taro, shine Iran ta amince da kiran Majalisar Ɗinkin Dunia, na wasti da mallakar makaman nuklea, wanda a sakamakon sa, za a cire takunkumin da a ka ƙargama mata.

To saidai tun kamin fara taron, shugaban tawagar Iran, ya sanar manema labarai cewar, ƙasar sa, na tsaye kan bakan ta, a dangane da wannan batu.

Ya ce ko da mafarki, Iran ba zata bada kai bori ya hau ba, wato saidai a kashe tsohuwa kan daudawar ta.