1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

180909 EU Finanzgipfel

September 18, 2009

Shugabannin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai EU sun ƙuduri aniyar ganin ƙasashen duniya sun yi aiki da wasu sabbin ƙa´idoji dangane da garaɓasar da ake bawa manejojin bankuna.

https://p.dw.com/p/JjRY
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firaministan Sweden Fredrik Reinfeldt a gun taron ƙolin EU na musamman a BrusselsHoto: AP

A wani taron ƙoli na musamman da suka gudanar a birnin Brussels shugabannin ƙungiyar sun amince da wata matsaya ta bai ɗaya game da ƙayyade yawan alawus alawus da ake bawa shugabannin bankuna, wanda za su gabatar a gaban taron ƙolin ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki a duniya da zai gudana a birnin Pittsburgh na ƙasar Amirka cikin mako mai zuwa.

Shugabannin ƙasashen ƙungiyar ta EU tuni suka fara hango taron ƙolin kan harkokin kuɗi na ƙungiyar G20 da zai gudana nan da mako guda a birnin Pittsburgh, domin a can ne za a tsayar da shawarwari game da batutuwan da EU ta amince da su a taronta na birnin Brussels. A taƙaice shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi bayani game da muhimmin batutuwan a gare ta kamar haka.

"Muhimmin abu a gareni shi ne na farko a kafa doka ta haramtawa banki ko wata cibiyar hada-hadar kuɗi matsawa gwanotoci lamba, na biyu shi ne ƙayyade ba da kuɗaɗen garaɓasa da samar da matsaya ta bai ɗaya na uku shi ne mu koyi darasi daga waɗannan matsalolin domin cimma wata madafa domin samun bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa."

To sai dai har suka kammala taron babu wani abu takamamme da aka gani kan waɗannan batutuwan. Maimakon haka sanarwa suka bayar kan jadawalin da za su gabatar a taron na birnin Pittsburgh. Alal misali ƙasar Austriya ta taɓo batun haraji ne kan duk wata hada-hadar kuɗi domin rage yawan ´yan baranda. Merkel na daga cikin shugabannin dake goyon bayan wannan shawara amma ta ce hakan zai yiwu ne a ƙarƙashin dokokin ƙungiyar G20. Shi kuwa Firaministan Sweden kuma shugaban EU a yanzu Fredrik Reinfeldt na ɗaya daga cikin shugabannin EU ƙalilan da suka nuna matuƙar adawarsu da wannan shawara.

"Bana jin wannan ita ce mafita. Abu mafi a´ala shi ne ƙasashe su ɗauki matakai na bai ɗaya akan kuɗaɗen garaɓasa da sa ido kan harkokin kuɗi da yin adalci. Wannan ita ce mafita."

Reinfeldt ya kasance mai gargaɗi cewa bai kamata shirye shiryen gwamnatoci na tallafawa tattalin arziki su zama na dindindin ba.

"Yanzu da tattalin arzikin duniya ya fara farfaɗowa ya zama wajibi mu kafa dokokin rigakafi. Dalilin shiga matsalar kuɗi shi ne dinbim basussuka dake kan ɗaiɗaikun mutane. Maganinsa ba shi ne ƙarawa ƙasa bashi kanta ba. saboda haka muke buƙatar matakan rigakafi."

To sai dai mafi rinjayen ra´ayoyi na goyon bayan ci-gaba da tallafawa tattalin arziki. Ko da yake dukkan ƙasashe 27 na tarayyar Turai sun halarci taron ƙolin na Brussels, amma kaɗan ne daga cikinsu wato masu ƙarfin tattalin arziki za su halarci taron na G20 a birnin Pittsburgh. Jerzy Buzek daga ƙasar Poland shi ne shugaban majalisar dokokin Turai, yayiwa manyan ƙasashen EU tuni game da nauyin dake kansu.

"Ya kamata a saurari koke-kokenmu a taron ƙolin na Pittsburgh. Yana da muhimmanci ƙwarai da gaske cewar ƙungiyar EU na wakiltar sauran ƙasashen da ba za su halarci taron na Pittsburgh ba."

A Pittsburgh EU za ta nuna ko za ta iya ƙarfafa matsayinta a tsakanin ƙasashen G20.

Mawallafa: Christoph Hasselbach/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Hauwa Abubakar Ajeje