1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Ecowas a Accra a can Ghana

Mansour Bala BelloJuly 30, 2004

Batun kasar Ivory coast shiya fi mamaye taron kasashen kungiyar Ecowas a Ghana

https://p.dw.com/p/Bvhe

Batun kasancewa dan kasa da kuma mutumin daya dace ya tsaya takara a kasar Ivory coast sune sukafi daukar hankali a taron da shugabannin kungiyar ta Ecowas keyi a kasar ta ghana bisa jagorancin MDd ..Wannan takaddanar dai shine makasudin haifar da yamutsi a kasar wanda ya nemi kuifar da gwamnatin shugaba Laurent bagbo a shekara ta 2002 .Bayan tattaunawa mai zafin gaske a jiya an dai gaza samar da wata mafita daya a dangane da wannan batu bisa laakari da kundin tsarin mulkin kasar ta Ivory coast .Har kawo yanzu dai tsugune bata kare ba a kasar duk kuwa da sanya hannun yarjejeniya a tsakanin yan tawayen kasar d a kuma Gwamnati a shekarar data gabata bisa lurqa ta musamman ga Uwar dakin kasar Faransa ..Babu shakka batun katin zama dan kasa da raban filaye na cikin baturtuwan dake cigaba da haifar da rudani a cikin kasar dake da alumma sama da miliyan 16 .Bugu da kari rahotanni na cewa yawancin bakin haure daga makwabtan kasashen na Ivory coast keda abun hannu fiye da wadanda ke ikirarin cewa sune yan asalin kasar ta Ivory coast .To sai dai kamar yarda daya daga cikin shugabannin yan tawayen kasar yace dole ne a tattauna batutuwan dake ciwa yan kasar tuwo a kwarya bisa tsare tsaren wanzar da zaman lafiyar da aka cimma a baya ...Yace gigitar dake dibar shugaba Bagbo a dangane da batun kundin tsarin mulkin kasar a yanzu ya zama sai tarihi bisa halin da kasar ta fada a ciki ..To sai dai manyan jamian dake halartar taron sun jadddda bukatar dake akwai na gudanar d a kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar domin bawa kowa ikon tsayawa takara a zaben shugabancin kasar a nan gaba a wani mataki na warware sarkakkiyar dake tattare da kasar a halin yanzu .Za dai a gudanar da wannan zabe a shekara mai kamawa a watan oktoba.Bugu da kari sun bukaci yan tawayen kasar su mika makaman su tare da shiga gwamnatin hadin kann kasa domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya mai dorewa ..A yanzu haka dai yan tawayen kasar sun mamaye arewacin kasar tare da barin kudancinta ga Gwamnati bisa shugabancin Laurent Bagbo .idan dai baa mantaba a wani sashi na kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa sai Mutum ya kasance gaba da baya dan asalin kasar ne kafin ya tsaya takara a shugabancin kasar wanda hakan ya haifar da haramtawa Pm kasar Alassan watarra tsayawa takara na neman shugabamncin kasar a shekara ta 2000.masu nazarin fannin sioyasar kasar dai sun tabbatar da cewa idan har baa dauki mataki ba a dangane da wannan tsarin da kasar ,ke kai a halin yanzu to babu shakka tsugune bata kare ba .To sai dai kamar yarda wani jammiin MDd a wannan taron yace da wuya wakilan taron su bawa Shugaba Bagbo goyan baya a dangane da wannan batu .To sai dai a daura da haka Kasar Faransa ta fara tunanin mika batun kasar a gaban kwamitin tsaro na MDd domin samun warakar data dace a nan gaba kadan .