Taron Duniya akan gangamin masifu | Siyasa | DW | 28.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Duniya akan gangamin masifu

An gabatar da taron yini uku domin nazarin matakan gangamin masifu daga Indallahi a nan birnin Bonn

Jan Egeland

Jan Egeland

A lokacin da yake jawabi gaban mahalarta taron Jan Egeland, wakilin MDD akan matakan taimakon jinkai, nuni yayi da cewar:

“Duk wata dala daya da zamu kashe akan matakan gagganmi da riga kafin masifu daga Indallahi zata samar mana da ribanyinta sau biyar, Ya-Allah mun kashe wannan dalar ce wajen dashen itatuwa ko shirye-shiryen ilimantarwa ko kuma wajen gina makarantu masu jure girgizar kasa. Dukkan wadannan matakai akan lura da amfaninsu ne bayan afkuwar wata masifa daga Indallahi, inda yawan kudaden da za a kashe wajen gyara bannar masifar ba zai taka kara ya karya ba.”

Bisa ga ra’ayi Jan Egeland dan kasar Norway riga kafi ya fi magani, kuma tilas a ba shi gaskiya a game da wannan batu idan an lura da ire-iren abubuwan da kan biyo bayan masifu daga Indallahi. Muhimmin matakin kadagarkin masufun kuwa shi ne gangami akan kari da kuma wani takamaiman shiri na tinkarar abin da zai biyo baya. Kuma ko da yake an samu kyakkyawan ci gaba a fasahar auna yiwuwar girgizar kasa, musamman ta amfani da bayanai na hutunan da taurarin dan-Adam ke aikowa, amma ana fama da gibi a harkar sadarwa domin wayar da mutanen dake zaune a yankunan da lamarin ya shafa a kan kari ta yadda zasu tsira da rayukansu, in ji Egeland, wanda ya kara da cewar:

“Ba shakka mun samu ci gaba a juyin-juya halin fasaha, musamman idan an yi batu a game da matakan gangami akan lokaci, amma har yau muna fama da gibi wajen gabatar da gangami ga jama’a. A saboda haka ba zamu iya zama mu harde kafafuwa ba sai bayan da muka cimma nasarar gabatar da gargadi ga dukkan masunta da manoma da masu hakan ma’adinai a game da bala’in da ka taso walau mahaukaciyar guguwar nan ce ta hurrican ko ambaliyar tsunami ko kuma girgizar kasa.”

Afurka dai na daya daga cikin yankunan dake bukatar irin wannan gangami ruwa a jallo, amma abin takaici shi ne yawo yanzu ba wand ke ba da la’akari da haka in ji jami’in na MDD.