1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Dumamar Yanayi

Abdullahi MaidawaDecember 4, 2007

Taimako zuwa ga kasashe masu tasowa

https://p.dw.com/p/CXA5
Klaus TöpferHoto: AP

Babban ƙalubale dake akwai yanzu shine yadda ƙasashen duniya da suka cigaba zasu rika bada tallafin su akai akai ga ƙasashen duniya masu tasowa ta fuskar raya muhalli, dashike waɗɗan nan ƙasashe dake tasowa sun shiga mawuyacin hali na gurbatawar muhalli ne sakamakon irin albarkatu da aka tono su wajen raya ƙasashen duniya da suke da arziki ta fuskar masana’antu, waɗɗanda kuma yau ake kira kasashe da suka cigaba.

Wani rahoto da shirin raya muhalli na majalisar ɗinkin duniya ( UNEP) ya fitar a wannan mako ya nunar cewa matsalar sauye sauyen yanani da matsalar fari, ko kanfan ruwa, biye da matsaloli na ambaliya ya tilasta mafi yawa cikin al’ummomin dake ƙasashe masu tasowa sauya rayuwar su zuwa cikin mawuyacin hali.

Me yiwuwa don wannan dalili ne masaniya ta fuskar muhalli dake kungiyar agaji ta Oxfam, na kasar Ingila Kate Raworth, cikin muƙalar data gabatar a taron na Bali, tace ƙasashe masu tasowa suna furkantar ƙuncin rayuwa domin kuwa basu samun taimakon daya kamata su riƙa samu .

ƙasashen dake yankin Asiya, sun sha fama da matsalolin talauci, Guguwar Iskar ruwa dakuma mace mace, baya ga hassarar dukiyoyi masu ɗimbin yawa sanadiyyar masifun da kan auka musu, to sai dai kuma taimako da suke samu ko kusa bai taka kara ya karya ba. ƙasashen Gambiya da Sudan dake nahiyar Afirka waɗɗanda ke fuskantar matsaloli ta fuskar sauye sauyen yanayi akai akai, dakuma fuskantar karancin ruwan sama,dakuma gurbacewar muhalli, zasu iya samun bunkasa ne daga matakin da suke na kashi 13 zuwa 37 cikin 100 na irin abubuwa da suke sarrafa su ƙarshen shekara ta fuskar anfanin gona, a bangaren Gambiya da kuma yakki da gugusowar Hamada a bangaren Sudan.

Don haka kenan yayinda masana suka hallara a taron na Bali, dake kasar Indonesia, mai samun mahalarta fiye da dubu ɗaya, daga sassan duniya baki daya, zai dace baya ga maye yarjejeniyar Kyoto dangane da ɗumamar yanayi kan shekartar ta dubu 2 da 12, zai dace ƙasashen da suka cigaba su duba hanyoyin taimakawa da kuɗaɗe don ceto kasashen dake tasowa da zummar taƙaita gurbatar muhallalinsu dakuma sama musu hanyoyi na ƙwarai da zasu kyaautata rayuwar su.