1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron dumamar yanayi a washinton

May 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuMV

A taron shekara shekara dake gudana a birnin washinton,kungiyar tarayyar turai da Amurka sun cimma matsaya guda dangane da mayar da fifiko wajen matsaloli dake tattare da dumamar yanayi.Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ,wadda kasarta ce ke rike da zagayebn shugabancin kungiyar ta Eu,ta bayyana cewa ya zamanto wajibi kasashe masu cigaban masanaantu suyi jagoranci ,wajen rage hayakin iska mai guba da manaantu ke fitarwa.Amurka dai tasha nuna halin ko oho adangane da rage hayaki mai guba da masanaantun kasar ke fitarwa.Bugu da kari bangarorin biyu sun kuma amince da wasu hanyoyin bunkasa tattali da harkokin ciniki.Sun kuma rattaba hannu a yarjejeniyar dake amincewa jiragen daukan kaya na kasashen turai suyi shawagi a sararin samaniyan Amurka,kana itama a bangarenta hakan,ayayinda a hannu guda kuma pasinjoji dake kasashen zasu ci moriyar farashi mai rahusa a tafiye tafiyensu.