1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron dumamar yanayi a Bali.

Halimatu AbbasDecember 6, 2007

Amurka ta nuna adawarta da rage hayaƙin masana'antu

https://p.dw.com/p/CYSs
mahalarta taron baliHoto: AP

Tawwagar Amurka a taron shawarta canjin yanayi da ke gudana a birnin Bali, ƙasar Indonesia, ta ce, Amurka ba za ta amince da rage hayaƙin masana’antu ba, duk da matsin lamba da ta ke fuskanta .

Wakilai daga ƙasashe kimanin 190 ke gudanar da wannan taro a birnin na Bali da nufin zayyana abin da zai kai ga sabon shirin shawo kan matsalar dimamar yanayi bayan ƙarewar wa’adin yarjejeniyar kyoto a shekara ta 2012.Kwararru sama da 200 biyu sun fid da shelarsu a taron, da ke yi kra ga rage hayaƙi mai guba da kashi 50 daga cikin ɗari nan da shekara ta 2050. Gaggan masana kimiya su kuma sun shiga wannan gwagwarmaya ta siyasa da ake yi akan canjin yanayi tare da yin kira ga alummanr duniya da su rage dimamar yanayi kwata kwata.Amurka dai a nata bangare sai kara yin kunnen uwar shegu ta ke yi ga waɗannan kiraye kiraye.Gabanin wannan taro sai da shugaba Bush ya nanata matsayin gwamnatinsa na ƙin amincewa da duk wata shawara da za ta nufaci rage hayaƙin masana’antu muddin za ta yi cikas ga ci gaban tattalin arziƙi.Shugaban tawwagar Amurka a taron na Bali Harlan Watson ya ce matakin da komitin majalisar dattawan Amurka ta dauka akan ƙayyade hayaƙin masana’antu, ko shawarar Australia ta sa hannu akan yarjejeniyar Kyoto ba za su canza matsayin Amurka a game da wannan lamari ba.

A ranar litini da ta gabata ne Prime ministan Australia Kevin Rudd ya sa hannu akan yarjejeniyar ta Kyoto. Kenan Amurka kadai ce ƙasa mai arziƙin masana’antu da ba ta rattaba hannu akan wannan yarjejeniya a shekarar 1997 ba.Wakilin Australia gun wannan taro ya ce sun ba da goyon bayansu ga sakamakon taron ƙasashe da su ka sa hannu akan yarjeniyar, da ya ba ƙasashe masu arziƙin masana’antu shawarar rage hayaƙin masana’antu da kashi 25 zuwa kashi 40 daga cikin ɗari nan da shekara ta 2020.

Ƙungiyar Tarayyar Turai ita kuma ta yi kira ga ƙasashe masu arziƙin masana’antu da su gano alhakinsu na jawo dimamar yanayi su kuma ba da goyon bayansu ga shirin rage hayaƙi mai guba da ke jawo dimamar yanayi.Watson ya ce Amurka ta na sa ran fitowa da matsayin ƙayyade hayaƙin masana’antu na ita kanta a taron ƙasashe 17da ke fid da hayaki mai guba da shugaba Bush zai jagoranta a shekara mai zuwa.