Taron Dumamar yanayi a Bali | Labarai | DW | 03.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Dumamar yanayi a Bali

A na cigaba da taron dumamar yanayi a tsibirin Bali dake ƙasar Indonesia.Taron wanda zai ɗauki kwanaki 11 yana gudana,na samun halartan ƙasashe sama da 180.Taro nada nufin ƙaddamar da tattaunawa adangane da yarjejeniyar da ake saran zata maye gurbin ta Kyoto,wadda wa’adin ta ke ƙarewa a 2012.Taron na tsibirin Balki dai ya samu karɓuwa,sakamakon yunkurin sabon prime ministan Australia Kevin Rudd na gyaran yarjejeniyar ta Kyoto,bayan rantsar dashi sakamakon zaɓen daya gudana a watan daya gabata.Yanzu dai ƙasar Amurka ce kadai,dake cikin kasashe masu cigaban masana’antu da har yanzu bata yi gyarn wannan yarjejeniya ta Kyoto.

Tawagar Amurka zuwa taron dai,ta nunar dacewa Washinton bazata zame ƙashin wuya adangane cimma sabuwar yarjejeniya kann sauyin yanayi ba,duk dacewa har yanzu Amurkan tana adawa da matakan da ƙasashe masu yawa suka amince dashi.