1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron duba ci-gaban shirin Millenium.

Yau, Majalisar Dinkin Duniya ka fara taron duba shirinta na Millenium a New York.

default

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon

A yau ne Majalisar Dinkin Duniya ke fara wani taro a birnin New York na kasar Amirka da zai samun halartan shugabannin 140, domin nazarin shirinta na Milleniunm da ya kuduri rage talauci a duniya nan da shekarar 2015. Babban sakataren Majalisa Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya ce ana bukatar karin kudi da kuma hobbasa ta hanyar siyasa. Sakamakon wani taro da ya gudana kafin wannan, ya bayyanar da cewa kasashe mawadata sun rage kudaden da suke bayarwa a matsayin taimako, sakamakon matsalar tabarbarewar tattalin arzikin duniya. Shirin na Millenium da aka kaddamar shekaru goma da suka gabata ba zai cimma manufarsa ba kafin karewar wa'adinsa. Manufarsa dai shi ne rage yawan wadanda ke fama da talauci a duniya da kashi 50 daga cikin dari da kuma yawan yaran da ke mutuwa kafin sun isa shekaru biyar da haifuwa, kafin shekarar 2015. Shugabar kungiyar UNESCO, Irina Bokova ta ce ana bukatar mai da hanakali ga manufar ba yaran mata ilimi, domin rage talauci. Ban a nasa bangaren cewa yayi kafin shekarar 2015 ana bukatar ba da fifiko ga shirin kula da yara da iyaye mata, da ke tafiyar hawainiya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Zainab Muhammad Abubakar