Taron Davos | Labarai | DW | 24.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Davos

Nan gaba kadan ne zaa bude taron manyan kasashen duniya da yan kasuwa kann tatalin arzikin duniya a wajen shakatawa na davos dake kasar Switzerland.

Taron dai zai duba batutuwa da dama da suka hada da canjin yanayi da kuma farfado da tatataunawar kungiyar ciniki ta duniya wadda ake samun sabanin raayin game da rage harajin kayayi.

Kimanin yan kasuwa da yan siyasa mawaka da yam jarida 2,400 ake sa ran zasu halarci taron,cikinsu da shugabanin kasashe 24 da suka hada da shugabar Jamus Angela Merkel wadda zata bude taron da kuma firaministan Burtaniya Tony Blair.