Taron dakile yaduwar cutar murar tsuntsaye a Senegal | Labarai | DW | 22.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron dakile yaduwar cutar murar tsuntsaye a Senegal

A yau ne za a fara taron kolin kasashe 15 na nahiyar Africa, dake cikin kungiyyar tattalin arzikin kasashen yamma, wato Ecowas a can Dakar babban birnin kasar Senegal.

Taron ,wanda za a gudanar dashi karkashin shugabancin Shugaba Abdoulaye wade na Senegal , an shirya shine da zummar samo bakin zaren dakile yaduwar cutar murar tsuntsaye ,wacce a yanzu ke barazana ga duniya.

Shirya wannan taro dai a cewar bayanai ya biyo bayan bullar cutar ne mai nau´in H5N1 a nahiyar ta Africa a can tarayyar Nigeria.

Mahalarta taron da suka fito daga cikin kasashen 15, an tabbatar da cewa zai sami halartar wakilan hukumar lafiya ta duniya da kuma ta kula da harkokin gona ta duniya.