Taron Copenhagen kan ɗumamar yanayi | Siyasa | DW | 08.12.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Copenhagen kan ɗumamar yanayi

Shugabannin ƙasashe kusan 100 ne ke halartar taron Copenhagen don cimma yarjejeniya ta yaƙi da sauyin yanayi a duniya.

default

Yvo de Boer, Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya kan yanayi

An buɗe babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan ɗumamar yanayi a birnin Copenhagen. Burin taron shine cimma yarjejeniya ta yaƙi da canjin yanayi, jama'a dama suna sa ran taron zai cimma nasara, sai dai kuma wasu na ganin cewa akwai yiwuwar kasa cin nasara a wannan taro.

Wajen buɗe taron dai babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya kan canjin yanayi, Yvo de Boer yace matakai da dama ne ya kamata a ɗauka don magance wannan matsala.

"Yanzu lokaci ya yi,bayan shekaru biyu na tattauna da ya kamata kwalliya ta biya kuɗin sabulu"

A fili dai yake cewa wannan shine taro mafi girma da aka taɓa gani, inda mutane 15,000 suke halarta, inda zasu kwashe makonni biyu suna tattauwa a babban birnin ƙasar Denmark, Copenhagen. Ba a dai taba samun babban taro da shugabannin ƙasashe da gwamnatoci fiye da 100 suka sanar da cewa zasu halarta ba, sai a wannan karon , saboda haka za a iya cewa wannan taro ne na duniya baki ɗaya.

Sai dai kuma abin takaici shine kafin wannan babban taro , wasu bayanan sirri da suka fito daga bakin masana kimiyar yanayi na Burtaniya, sun nuna cewa, an ƙara gishiri cikin sakamako wasu bincike kan yanayi da aka gudanar domin ƙara janyo hankalin jama'a game da illar ɗumamar yanayi. Masu sukar batun ɗumamar yanayi suna adawa da cewa mutum shi ke da alhakin ɗumamar yanyin, amma kuma irin waɗannan mutane ƙalilan ne. Koma dai menene sakamakon bincike da aka gudanar, batun guda ɗaya ne dukkan hankula sun karkata alƙibla guda, wato dole ne a yi wani abu game da canjin yanayi, ba ma saboda mu ba ƙadai saboda 'ya'yayenmu da kuma suma 'ya'yayensu.

Mutane ne dai musamman ma na ƙasashe da suke da arzikin masana'antu suke ƙara gurɓata yanayi saboda neman ci gaba. To sai dai kuma abinda suka manta shine babu isasahen fili a duniya da zai kwashi dukkan gurɓattacen hayaƙin carbon da ake tuttuɗawa zuwa sarararin samaniya. Kamar yadda ake biyan kuɗin kwashe datti ya kamata a keɓe kuɗi da za a rinƙa kula da wannan gurɓattaccen hayaƙi. Kodayake idan babu sinadarin carbon a duniya rayuwa ba zata yiwuwa ba, amma kuma idan ya yi yawa za a samu tsananin zafi ta yadda kuma rayuwar ba zata yiwu ba. Kuma illar wannan bau ta fi shafar mafi yawancin ƙasashen da bazasu iya yin komai akai ba. Saboda haka yaƙi da dumamar yanayi yaƙi ne kuma na neman yin adalci.

BdT Deutschland Klima Energie Kohle Kohleverstromung Schwarze Pumpe

Hayaƙin Masana'antu

Rawa da kowane ɓangare zai taka dai a baiyana yake, dole ne ƙasashe da ke da arzikin masana'antu su ɗaukin nauyin kuɗi na magance wannan matsala da suka haddasa. Su gagauta fitar da kudi da kuma samar da kimiyar rage wannan matsala. Su kuma ƙasashe dake neman ci gaban masana'antu sai su shafawa gemunsu ruwa, don kada su yi kuskure irin na ƙasashe da ke arzikin masana'antun.

Ya kamata taron na Copenhagen ya samu nasara saboda rayuwar kowane mutum a doron ƙasa, ko da kuwa daga ina ya fito, Indiya ne, Rasha, Jamus ko Najeriya kowane ɗan Adam yana da 'yancin shaƙar kyakkyawar iska. Wannan matsala ce dake bukatar taimako daga dukkan alummomin duniya fiye da yadda ake zato. Yvo De Boer yace ta gagauta ɗaukar mataki ne kaɗai za a iya samun nasara.

"hanya kadai da za a iya samun nasara a Copenhagen itace, idan taron ya samar da hanyoyin na daukar matakan gaggawa masu ma'ana, waɗanda zasu fara aiki tun daga ranar da wannan taro ya kamala"

A taruka kan ɗummar yanayi na baya dai, an fi maida hankali ne kan muhalli. Ya kamata wannan taro da ya haɗa kan manyan shugabannin ƙasashe fiye da 100, ya samar da yarjejeniya, idan kuwa ba a cimma yarjejeniyar ba, wannan zai iya kasancewa taron siyasa da ya fi kowanne rashin samun nasara a tarihin duniya.

Mawallafi: Hauwa Abubakar Ajeje

Edita: Umar Aliyu