Taron Cairo yayi kira ga janyewar sojojin Habasha daga Somalia | Labarai | DW | 04.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Cairo yayi kira ga janyewar sojojin Habasha daga Somalia

Jamian diplomasiya na Amurka Turai da kuma a Arika da suka gana kan halinda ake ciki a kasar Somalia sunyi kira ga janyewar dakarun Habasha daga kasar ta Somalia .

Sun kuma kira da a tattauna tsakanin bangarori dake yaki da juna.

Ministan harkokin wajen Norway Raymond Johansen yace ya kamata sojojin Habasha su janye ba tare da bata wani lokaci ba.

Kodayake sun bukaci aikewa da karin sojoji na AU kimanin 8,000 zuwa kasar ta Somalia .

Yanzu haka dai kasar Uganda ce kadai ta aike da dakarunta karkashin AU,kodayake kasashen Burundi da jamhuraiyar Benin sun alkawarta aikewa da nasu dakaru amma sunce suna bukatar lokaci.

Tashe tashen hankula mafiya muni tun shekaru 15 sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama musamman a birnin Mogadishu.