Taron bita na majalisar ministocin Jamus | Siyasa | DW | 11.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron bita na majalisar ministocin Jamus

A jiya talata ne majalisar ministocin Jamus ta kammala taronta na bita na farko domin nazarin manufofin gwamnati

Taron bitar dai an gudanar da shi ne a bayan fage kuma da kyar aka samu sulalewar wasu ‚yan bayanai daga zauren taron. A sakamakon haka aka samu cunkoson ‚yan jarida a taron manema labarai da ya biyo baya. A hadin guiwa da mataimakinta Franz Münterfering, shugabar gwamnati Angela Merkel ta gabatar da sakamakon taron bitar na majalisar ministocinta tana mai cewar:

Babbar manufar da muka sa gaba da farkon fari shi ne na kyautata yanayin dangantaka da karfafa yarda da juna tsakanin wakilan gwamnatin ta hadin guiwa. Domin wannan shi ne muhimmin sharadin samun kafar gudanar da ayyukan gwamnatin ba tare da wahala ba.

Wannan bayanin na Angela Merkel na mai yin nuni ne da fafutukar da ‚yan Christian Union da Social Democrats ke yi na dinke barakar dake tsakaninsu akan wasu muhimman batutuwan da suka hada da garambawul ga manufofin kiwon lafiya da kasuwar kodago da janyewa daga makamashin nukiliya, wadanda ba a tabo su a zauren taron ba. A maimakon haka aka mayar da hankali akan batutuwan da ba wani sabani tsakanin sassan biyu. Merkel ta kara da bayani tana mai cewar:

Mun mayar da hankalinmu ne akan batutuwan dake da muhimmanci a halin yanzu. Wannan maganar musamman ta shafi hanyoyin ta da komadar tattalin arzikin kasa da samar da guraben aikin yi ga jama’a. A wannan bangaren muke fatan cimma nasara akan manufa.

Gwamnatin na da niyyar kashe abin da ya kai Euro miliyan dubu 25 domin daidaita al’amuran tattalin arzikin Jamus a cikin shekaru biyar masu zuwa. Wadannan kudaden za a yi amfani da su ne a harkar binciken kimiyya da fasaha sai kuma hanyoyi na sufuri da kyautata zamantakewar iyali. Kazalika gwamnati na da niyyar rufa wa masu sana’o’in hannu da kamfanonin gine-gine baya. Sai dai wadannan batutuwan ko kadan basu gamsar da ‚yan hamayya ba, kamar yadda aka ji daga bakin Claudia Roth shugabar jam’iyyun kawance na The Greens da Alliance 90, ta kuma kara da cewar:

Wannan wata hadin guiwa ce dake cika baki ba tare da tabuka kome ba. Dukkan abubuwan da suka fada ba tabbas game da su. Dukkan sassan biyu sun kasa shawo kann ainifin sabanin da suka sha fama da shi a ‚yan makonnin baya-bayan nan. Cece kuce ne kawai suke yi ba tare da cimma bakin zaren warware matsalolin dake akwai ba.

Shi ma shugaban jam’iyyar Free Democrats Gudo Westerwelle ya bayyana tababarsa a game da cewar wannan shiri, wanda ya tanadi Euro miliyan dubu 25 zai taimaka wajen samar da isassun guraben aikin yi ga jama’a. Amma Merkel da mataimakinta Münterfering sun sikankance cewar wadannan kudade zasu taimaka wajen ta da komadar tattalin arzikin Jamus.