1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron birnin Paris don taimakawa Falasɗinawa

Ƙasashen duniya sun yi alƙawarin ba Falasɗinu dala miliyan dubu 5.6

default

Shugaba Mahmud Abbas

Ƙasashen duniya sun shirya ba da taimakon dala miliyan dubu 5.6 har tsawon shekaru uku don inganta halin rayuwa da ya taɓarɓare a yankunan Falasɗinawa. Hakan na ƙunshe a cikin wani shiri wanda Firaministan Falasɗinawa Salam Fayyad ya mika shugaba Mahmud Abbas, kuma ya ke matsayin ajandar taron na ƙasa da ƙasa a birnin Paris.

Taron da ke samun halarcin wakilan ƙasashen kimanin 90 ba batun taimakon gaggawa ga Falasɗinu kaɗai ne zai tattauna kai ba a´a ya na da kuma nufin taimakawa shirin samar da zaman lafiyar yankin Gabas Ta Tsakiya wanda aka sake farfaɗo da shi a taron birnin Annapolis din Amirka ƙarshen watan nuwamba. Dukkan waɗanda abin ya shafa sun san cewa ba za´a iya rarrabewa tsakanin zaman lafiya da kuma wata wadata ta tattalin arziki komun ƙanƙancinta ba.

Tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair wanda ke zama wakilin ɓangarorin hudu dake shawarta batun zaman lafiyar Gabas Ta Tsakiya tare da sake gina hukumomin gwamnatin Falasɗinu shi zai shugabanci wannan taro. A lokacin da ya kai wata ziyara a gabar Yamma da Kogin Jordan ya nuna kyakyawan fata ya na mai cewa.

Blair:

“Muna samun ci-gaba a ayyukan farfaɗo da tattalin arziki, musamman ga al´umar Falasɗinawa waɗanda ke son su gani irin wannan ci-gaba a kasa musamman don samun guraben aikin yi, wadata da kuma inganta halin rayuwarsu. Ga isra´ila kuwa dole a tabbatar mata da tsaro da zaman lafiyar ta.”

Yunƙurin farko na maido da tattaunawar samar da zaman lafiya bisa turba bai samar da sakamakon da aka yi fatan samu ba. Har yanzu ana cikin wani mawuyacin hali sakamakon gwagwarmayar rike madafun iko tsakanin kungiyar Hamas wadda ta shafe watanni tana iko da Zirin Gaza da kuma kungiyar fatah dake ko da Yammacin Kogin Jordan karkashin jagorancin Abbas da Fayad. Ko da yake dukkan su biyu na son kare bukatun mazauna Zirin Gaza kimanin miliyan daya da rabi amma a zahiri hakan ba mai yiwuwa ba ne. Saboda haka a matakin farko kuɗaɗen da taron an Paris zai tara za´a fara taimakawa yankin Yammacin Kogin Jordan ne. Baya ga kuɗaɗen da bankin duniya da kuma asusun IMF suka yi alkawarin ba wa gwamnatin Firaminista Fayad, ita ma Amirka ta ninka taimakon da take bawa Falasɗinu har sau uku ya zuwa dala miliyan 400 a baɗi. To sai dai taimakon kudi kaɗai ba shi ne mafita ba, dole ne Isra´ila ta kawo ƙarshen tarnaƙin da take yiwa yankunan Falasɗinawa.