Taron birnin Amman kan yan gudun hijira na Iraqi | Labarai | DW | 26.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron birnin Amman kan yan gudun hijira na Iraqi

Kasar Jordan ta roki taimakon kasashen duniya wajen kula da dubban yan gudun hijira na Iraqi dake kasar a wajen wani taro da aka bude yau kann halinda yan gudun hijira na Iraqi su fiye da miliyan 2 da suka tserewa yaki a kasarsu.

Sakatare janar na maaikatar harkokin cikin gida na Jordan Mukheimer Abu Jamous ya fadawa taron cewa yan gudun hijira na Iraqi su 750,000 a cikin kasar ta Jordan sun janyo matsaloli musamman kann ababen kula da jin dadin rayuwa a kasar.

Haka kuma Jordan ta baiyana damuwarta game da yiwuwar barkewar rikicin sunni da shia a cikin kasar tata.