1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Neman mafita kan rikici

January 16, 2020

A kokarin ganin sun kawo karshen rikicin da ake fama da shi a kasar Libiya, kasashen duniya tare da tallafin Majalisar Dinkin Duniya, za su yi zama na musamman a Berlin domin warware matsalar.

https://p.dw.com/p/3WIsi
Bildkombo Haftar und as-Sarradsch
Jagoran 'yan tawayen Libiya Khalifa Haftar da shugaban kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi Fayez Sarraj

Zaman na Berlin zai hada kan firaministan kasar ta Libiya Fayez Sarraj da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kuma wasu kasashen yamma ciki har da Jamus da kuma bangaren Janar Khalifa Haftar wanda dakarunsa ke kokarin karbe ikon kasar. Hawa teburin sulhun da ake kokarin yi dai, wani yunkuri ne na ganin an cimma matsaya bayan da aka gaza samun daidaito a zaman da aka yi a birnin Moscow na kasar Rasha. Bayan kammala taron na Moscow dai, Janar Haftar ya ki sanya hannu kan yarjejeniyar da aka cimma, wanda masana irinsu Andreas Dittmann da ke jami'ar Justus-Liebig-University Giessen da ke Jamus suka alakanta da fargaba da bangarensa ke da ita ta rasa karfin iko a sassan kasar daban-daban.

Matsalar kungiyoyin masu dauke da makamai

Baya ga wannan batu, akwai kuma magana ta kananan kungiyoyi da ke dauke da makamai wadanda ke goyawa gwamnatin Tripoli baya da kuma bangaren Haftar din ke ganin muddin suka sassauto daga matsayin da suke kai, to kungiyoyin ka iya samun karfin murkushesu duba da yawansu da kuma karfin da suke da shi. In har hakan ta afku, bangaren Sarraj ka iya kara samun tagomashi da kuma karbuwa a idanun kasashen duniya da ke goya masa baya.

Libyen zerstörtes Gebäude in Tripoli
Yaki na ci gaba da ragargaza LibiyaHoto: Imago

Yayin da wasu ke tsokaci kan wannan yanayi da za a iya shiga idan bangaren Janar Haftar din ya sassauto, wasu na ganin lamarin fa ba haka yake ba duba da irin goyon bayan da bangaren nasa ke samu daga kasashe kamar Rasha da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Faransa. Irin wadannan kasashen da ke bayansa ne ya sanya Tim Eaton masanin kan harkokin arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya a cibiyar nan ta Chatam House da ke Birtaniya, ke ganin da kamar wuya ya bukaci tallafi daga wasu kungiyoyi.

"Haftar na da makusanta cikin kasashen duniya, wanda hakan ya bashi dama ta iya yin watsi da duk wani tayi daga wata kasa. Sai dai yanzu hankali ya karkata kan yadda za ta kaya tsakaninsa da Putin kasancewar ya yi watsi da kasarsa a wancan zama da aka yi."

Yanzu haka dai al'ummar Libiya da ma na kasashen duniya da ke bibiyar halin da ake ciki, na zuba idanu domin ganin abin da wannan zama na Jamus din zai haifar, musamman ma da yake kasashen da ke mara musu baya gami da kungiyar kasashen Afirka ta AU sun amince su tura wakilansu wajen taron. Sai dai wasu na ganin zaman zai fi armashi ne idan har Firaminista Sarraj da Janar Haftar suka halarci zaman da kansu.