Taron Bali na fuskantar turmin-danya | Labarai | DW | 13.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Bali na fuskantar turmin-danya

An cimma turmin danya a tsakanin Ƙungiyyar Tarayyar Turai Eu da ƙasar Amirka, a game da batun kare muhalli. Amirka dai taƙi sa hannu kann yarjejeniyar rage gurɓataccen hayaƙi da kamfaninnikan ƙasar ke fitarwa da kashi 40 cikin ɗari, daga nan izuwa shekara ta 2020.Ƙungiyyar tarayyar Turai ta ce hakan babban tarnaƙi ne ga burin da ake son cimma na kare muhalli.A jawabin daya gabatar jiya, sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Mr Banki Moon ya ɓukaci mahalarta taron tsara wani daftari da zai maye yarjejeniyar ɗumamar yanayi ta birnin Kyoto, da amfaninta ke ƙaraewa a 2012. Gaza cimma matsaya guda a game da matsalar ɗumamar yanayin a cewar Banki Moon , abune da ka iya jefa Duniya cikin wani hali na ƙaƙa ni kayi. Kafafen yaɗa labarai sun rawaito wakiliyar Amirka a taron, Paula Dobriansky na watsi da zargin da akewa Amirka.