Taron baje kolin kayan tarihi da al´adu | Zamantakewa | DW | 02.07.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taron baje kolin kayan tarihi da al´adu

Taron baje kolin ya samu halarcin dukkan waɗanda ke da ruwa da tsaki a harkar kayakin tarihi da na al´adu na Afirka

default

Kayan sassaƙa na tarihi a Afirka

Aƙalla ƙasashen Afirka 40 ne suka halarci wani taron baje kolin kaakin tarihi da fasahar ƙereƙere na al´adu na ƙasashen Afirka karo na biyu a Abuja babban birni tarayyar Nijeriya mai taken samo kafar amfani da kayakin tarihi da al´adu domin rage raɗaɗin matsalar tattalin arziki da yanzu haka ta addabi duniya baki ɗaya.

Hakazalika taron ya samu halarcin ministoci dake kula da harkokin tarihi da al´adu na ƙasashen Afirka 10 kuma ya bawa wasu ƙasashen duniya musamman daga nahiyoyin Turai da Asiya damar zuwa domin kashe kwarkwatar idanunsu. Ra´ayin mahalarta kasuwar baje kolin ya zo ɗaya cewa fannin kayakin tarihi da al´adu idan aka bunƙasa su to za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasashenmu na Afirka.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin