Taron Babbar Mashawartar Majalisar Dinkin Duniya | Siyasa | DW | 20.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Babbar Mashawartar Majalisar Dinkin Duniya

A gobe talata ne za a fara taron babbar mshawartar MDD a birnin New York, inda ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ke fatan yin amfani da wannan dama domin yayata bukatar kasar ta samun dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu na majalisar

Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer

Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer

A matsayinta na kasa ta uku dake ba da gudummawa mafi tsoka ga kasafin kudin MDD Jamus na da kyakkyawar dama ta samun dawwamammen wakilci a kwamitin sulhun majalisar, musamman ma ganin yadda take shiga ana damawa da ita a manufofi na siyasa da matakai na kiyaye zaman lafiyar MDDr yanzu haka. Samun irin wannan wakilci na dindindin abu ne da zai taimaka kasar ta Jamus tayi tasiri, saboda ta haka zata samu ta cewa kai tsaye a duk wata shawarar da kwamitin na sulhu zai tsayar. Domin kuwa ba dukkan shawarwarin da kwamitin ke yankewa ne suka jibanci batutuwan tsaro ba, kazalika da yawa daga cikin shawarwarin nasa suna da nasaba da manufofin tattalin arziki, kuma Jamus ba zata yarda ta zama ‚yar rakiya a wasu kudurorin kwamitin da ka iya zama illa ga makomar tattalin arzikinta ba. Kasar dai tana samun goyan baya daga akasarin kasashen MDDr su 190, musamman ma daga rukunin kasashen dake da irin wannan buri na samun kujera ta dindindin a kwamitin sulhu, kamar Indiya da Brazil da kuma Japan. Ita ma Amurka ko da yake ba ta ce uffan ba, amma mai yiwuwa ta ba da goyan baya a cewar Klaus Hüfner, kwararren masani akan al’amuran MDD. Ainifin masu adawa da wannan manufa wasu ne daga cikin kawayenta na nahiyar Turai, kamar Italiya, wacce take ganin za a mayar da ita tamkar wata kasa mai daraja ta biyu, idan har Jamus ta samu irin wannan kujera, a baya ga kasashen Birtaniya da Faransa. A sakamakon haka gwamnatin Italiya ke bakin kokarinta wajen hana ruwa gudu bisa manufa. Da dai so samu ne da kuwa ita Jamus zata fi kaunar ganin an ware wata kujera bai daya da za a ba wa illahirin kasashen kungiyar tarayyar Turai, amma tuni gwamnatin hadin guiwa ta SPD da the Greens ta soke wannan maganar daga cikin manufofinta saboda ba abu ne da zai samu ba. Bugu da kari kuma shi kansa ainifin kudurin MDD bai tanadi wata kafa ta ba wa wani gungu na kasashe wata dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu ba. Amma duk da haka ana nan ana nazarin shawarwarin garambawul da sakatare-janar Kofi Annan ya zayyana, wanda kuma za a gabatar a zauren taron MDDr a farkon watan desamba mai zuwa. Babban abin da ake fata a game da wannan garambawul shi ne ba wa MDD wani safifin fasali na magana da yawun kowa-da-kowa ba tare da fifita wasu kasashen akan wasu ba. Abin da Jamus ke fargaba shi ne rashin nasarar wannan manufa ta garambawul, domin kuwa tilas ne manufar ta samu goyan baya na kashi biyu bisa uku na wakilanta da kuma dukkan wakilai biyar dake da dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu. Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka gabatar da yunkurin kawo canji ga tsare-tsaren kwamitin sulhu na MDDr ba, kuma ba shakka za a sha fama da zazzafar mahawar akan wannan manufa.