Taron Ba Zata Na Ministocin Harkokin Wajen Kasashen KTT | Siyasa | DW | 03.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Ba Zata Na Ministocin Harkokin Wajen Kasashen KTT

A yammacin jiya talata ministocin harkokin wajen kasashen KTT suka gudanar da taronsu a Brussels, inda suka amince a game da ba wa Iraki kakkarfan taimako

Wani abin lura a game da taron na ministocin harkokin wajen kasashen KTT shi ne kasancewar ba su tabo maganar hukumar zartaswa ta kungiyar ba, wacce a halin yanzu haka ake sabani a game da tawagar da sabon shugabanta Jose Manuel Barroso ke da niyyar nadawa. An saurara daga bakin ministan harkokin wajen jamus Joschka Fischer yana mai bayanin cewar wannan maganar ba a shigar da ita a ajendar taron ba, ko da yake wannan batu ya sha kan dukkan ministocin na harkokin waje. Babban abin da ministocin suka mayar da hankali kansa shi ne halin da ake ciki a Iraki da yankin gabas ta tsakiya, inda suka tsayar da shawarar ba da cikakken goyan baya ga gwamnatin wucin gadi ta kasar Irakin, kamar yadda aka ji daga bakin ministan harkokin wajen kasar Netherlands Bernhard Bot, wanda ya kara da cewar:

Mun tsayar da shawara akan wasu tsayayyun matakai na taimako, abin da ya hada har da tallafi na kudi dangane da zaben da aka shirya gudanarwa a cikin watan janairu mai zuwa. Ba’ada bayan haka za a tura wata tawagar Kungiyar Tarayyar Turai domin bin bahasi akan irin gudummawar da za a iya bayarwa wajen ba da horo ga jami’an ‚yan sanda da kuma karin ilimi akan al’amuran shari’a.

Dangane da matakai na matsakaicin lokaci kuwa, ministocin harkokin wajen sun dace akan shiga tattaunawa domin kulla wata yarjejeniyar ciniki tare da kasar Iraki. A nasa bangaren ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya fito fili ya bayyana cewar duka-duka taimakon da kasar zata iya bayarwa ya shafi manufofi ne na farar fula. sannan ya ci gaba da cewar:

Maganar ta shafi irin gudummawar da zamu iya bayarwa ne a manufofi na farar fula domin tabbatar da zaman lafiya da sake gina kasar Iraki. Jamus dai har yau tana kan bakanta na kin tura dakarun soja zuwa kasar ta Iraki. A halin yanzu haka kasar na ba da horo ga jami’an ‚yan sandan Iraki a wajen kasar. Sai kuma nan gaba a yi bitar maganar shari’a da sauran batutuwan da suka shafi farar fula.

Ministocin harkokin wajen na kasashen KTT su 25 sun duba halin da ake ciki a yankunan dake karkashin mamayen Isra’ila ta la’akari da rashin lafiyar shugaban Palasdinawa malam Yassir Arafat. Sun yaba da kokarin da Palasdinawan ke yi na lafar da kurar da ake fama da ita bayan fitan Arafat zuwa neman magani a kasar Faransa.