1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron AU kan aikewa da dakaru zuwa Somalia

Kungiyar taraiyar Afrika AU a yau take bude wani taro na musamman akan batun aikewa da dakarunta zuwa Somalia,yayinda wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya kuma ya isa birnin Mogadishu a kokarin sasanta rikicin kasar.

default

Taron na komitin tsaro na kungiyar AU da zaa fara yau a birnin Addis Ababa na kasar Habasha zaiyi muhawara kan sabon rahoton halinda ake ciki yanzu a kasar Somalia tare da nufin yanke shawar kan aikewa da dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa kasar.

Ya zuwa yanzu dai kasar Habasha wadda dakarunta suke kasar bayan korar shugabanin kotunan musulunci daga kasar,tace tana son janye dakarun nata sai dai kuma tace bata samu wata nasara ba,a kokarin da takeyi ita da kasar Kenya na janyo hankalin kasahen su bada gudumowar nasu dakaru zuwa Somalia,inda Uganda ce kadai kasa data bada gudumowar dakarunta.

Afrika ta kudu daya daga cikin kasashe da aka nemi su bada dakarun nasu ta baiyana shakkunta kan ko dakarun na AU zasu iya daukar nauyin wani aikin wanzar da zaman lafiya kan wanda take gudanarwa yanzu a kasashe kamar Sudan.

Wani kwararre kuma kan harkokin Somalia a cibiyar nazarin harkokin tsaro dake Pretoria ATK Richard Cornwell yace yana ganin da kyar ne a samu nasara a wannan bangare inda a cewarsa tun kafa gwmantin wucin gadi ake batun aikewa da dakaru zuwa Somali

Yace shekaru da dama ake maganar aikewa da dakarun AU da IGAD,tun lokacinda aka kafa gwamnatin wucin gadi a 2004 tunda bata da dakaru na kanta,nan take shugaban kasa Abdullahi Yusuf ya aike da bukatar taimako na kudi da soji na kasa da kasa,wanda kuma bai samu ba,kuma kawo batun yaki da taaddanci da wargajewar kasar a wannan karo,yana ganin zai zabura kasashe su kawo masa dauki,muddin kuwa bai baiyana yadda dakarun zasu kasance ko aiyukan da zasu ba a Somalia,bana ganin alkawuran tainako da akeyi zai tsinana wani abu.

Gwamnatin wucin gadin ta Somalia tunda aka kafa ta tana zama ne a Baidoa,bayan madugan yaki dake da goyon bayan Amurka suka maamye harkokin kasar wadanda daga bisani magoya bayan kotuan musulunci suka kora suka kuma maido da doka da oda,sai kuma bayanda dakarun Habasha suka kori shugabanin kotunan islama tukuna suka koma Mogadishu.

Shugaban na Somalia ya sake mika kukansa musamman ga Amurka data taimaka wajen gina mata rundunonin soji dana yan sanda tare da harkokin liken asiri.

Majalisar dinkin duniya a nata bangare tace yanzu lokaci ne da Somalia kanta zata dinke baraka dake tsakanin alummominta.

Wakilin musamman na sakatare janar na majalisar Francois Fall da yanzu haka ke Mogadishu ya gana da shugabanin Somalia yace yanzu lokaci ne da bangarorin kasar zasu sasanta sai dai yayi suka ga sauke kakakin majalisa Sharif Hassan Sheikh Aden ana zarginsa da goyon bayan kotunan musulunci.

 • Kwanan wata 19.01.2007
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwY
 • Kwanan wata 19.01.2007
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwY