Taron AU da makomar dakarun kiyaye zaman lafiya | Labarai | DW | 10.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron AU da makomar dakarun kiyaye zaman lafiya

Shugabannin kungiyar gamaiyar Afrika na gudanar da taro taro a birnin Addis Ababa domin yanke shawara a game da makomar dakarun kiyaye zaman lafiya na AU dake lardin Dafur na kasar Sudan. A rahoton sa Shugaban hukumar gudanarwar AU, Alpha Omar Konare ya bada shawarar tsawaita aikin dakarun na AU da kimanin watanni tara, hakan dai zai dogara ne ga yadda kungiyar ta AU ta sami taimakon kudi daga takwarorin ta don gudanar da aikin dakarun sojin. Kungiyar AU wadda ke da dakarun kiyaye zaman lafiya 7,000 a lardin Dafur na fama da karancin kudaden tafiyar da aikin sojojin. Ministan harkokin wajen Sudan Lam Akol yace shawarar kungiyar gamaiyar Afrika na mika ragamar gudanarwar dakarun kiyaye zaman lafiyar ga majalisar dinkin duniya zai kawo karshen tattaunawar samar da zaman lafiya da ake gudanarwa a Nigeria da ma kuma dukkan wani batun shaánin tsaro na kungiyar ta AU. Amurka da kungiyar tarayyar turai na yin matsin lamba ga kasar Sudan ta amince da dakarun sojin kiyaye zaman lafuiyar na majalisar dinkin duniya.