Taron AU da EU ya cimma yarjejeniya akan batun bakin haure | Labarai | DW | 24.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron AU da EU ya cimma yarjejeniya akan batun bakin haure

Taron ministocin kasashen taraiyar Turai da Afrika a Libya ya cimma wata yarjejeniya kann batub bakin haure da zai taimaka kaiwa ga cimma nasara a fanonin ci gaba da kuma matakan tsaro.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa bangarorin byiu sunce ba zai yiwuwa a magance matsalar bakin haure ta hanyar tsaro ba kadai.

Suna masu jaddada tabbatar da kawadda talauci,rashin aikin yi da cututtuka tare da bullo da hanyoyin ci gaba.

KTT dai ta mika tayin kirkiro da wani tsari na baiwa wasu kayaidaddun masu kaura damar shiga turai bisa bukatar da take da ita a kasuwar kodago a kowace shekara.

Hakazalika tayi alkawarin kara taimakon da take bayarwa ga nahiyar da karin 0.56 na bainda take samu nan da 2010 da kuma wani karin da 0.7 zuwa 2015.