Taron asusun taimako na kasa da kasa a Berlin | Siyasa | DW | 27.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron asusun taimako na kasa da kasa a Berlin

Manyan wakilai 50 ake sa ran zasu halarci taron asusun taimako na kasa da kasa a birnin Berlin

Bahaushe dai ya kan ce: “Ba girin-girin ba, tayi mai” ba kawai a rika gabatar da alkawururruka na fatar baki ba, muhimmin abu shi ne a rika cika su, a saboda haka Helle Jeppesen take cewa duk wata kyakkyawar niyya da mahalartar taron su kimanin 50 zasu nunar ba zata tsinana kome ba muddin ba a cika wannan niyya ba, domin ta haka ne kawai za a tabbatar da cewar wakilan na gwamnati da ‘yan kasuwa da kungiyoyi masu zaman kansu da gaske suke a game da kyautata makomar kiwon lafiyar dan Adam a duniya baki daya. Ana fata, taron wanda shi ne na biyu da asusun taimako na kasa da kasa ya shirya, zai tara abin da ya kai tsabar kudi dala miliyan dubu bakwai zuwa dubu takwas domin yaki da cuttuka irinsu Aids da zazzabin cizon sauro da tarin fuka. Wannan shi ne gangami mafi girma irinsa da aka taba fuskanta a cikin tarihi domin tabbatar da kiwon lafiyar jama’a kuma babban ci gaba a shirin nan da ya tanadi manufofin MDD dangane da shekaru na dubu biyu.

A shekara ta 2002 ne aka kirkiro wannan asusu domin yakar cututtukan na Aids da zazzabin cizon sauro da tarin fuka a duk fadin duniya. Maganar a takaice ta shafi wata manufa ce ta kiwon lafiya a kasashen da wadannan cututtuka ke yaduwa a cikin hamzari, kazalika da manufofi na biuncike da daukar matakai na riga kafi, wadda aka ce ta fi magani. Bahaushe ya ce lafiya uwar jiki, amma a saboda rashin lafiya mutane masu tarin yawa a sassan duniya daban-daban ba su da karfin yin aiki ballantana su samu kudin sayen magunguna. Akwai dai dalili game da kwarin guiwar cewa taron zai haifar da da mai ido idan an yi la’akari da ire-iren ci gaban da aka samu tun bayan kirkiro asusun taimakon na kasa da kasa a shekara ta 2002. Asusun na taka muhimmiyar rawa matuka ainun wajen yakar cututtuka masu yaduwa a sassa daban-daban na duniya yanzu haka, inda yake daukar nauyin kashi daya daga cikin biyar na yawan kudaden da ake kashewa wajen yaki da cutar Aids da kuma kashi daya bisa uku na abin da ake kashewa akan cututtukan zazzabin cizon sauro da tarin fuka. Tun bayan kafa shi a shekara ta 2002 asusun taimakon na kasa da kasa ya kashe jumullar kudi na dala miliyan dubu takwas da dari shida a matakan kiwon lafiya a kasashe 136, ko da yake har yau da sauran rina a kaba kafin a cimma biyan bukata kwata-kwata. A yayinda kasashen G8 ke fatan gabatar da magunguna ga dukkan masu cutar Aids a sassa daban-daban na duniya nan da shekara ta 2010, ita kuma MDD fata take yi ta kayyade yawan masu kamuwa da da cutar tarin fuka da ta zazzabin cizon sauro da misalin kashi 50 cikin dari na da shekara ta 2015. A saboda haka abin fata shi ne ka da taron na Berlin ya tsaya kan alkawururruka na fatar baki kawai.